12/04/2024
Dawwama akan aikin alkhairi kashi na farko (1)
------------------------------------
Dukkan wanda Allah (S.W.T.) yai masa damkatar dayi masa biyayya da kuma aikata ayyukan alkhairi acikin wataran Ramadan haƙiƙa Allah ya datar dashi da mafi girman falala. Sai dai babban ƙakuban shi ne dawwama akan aikin.
Mutane da yawa su kanyi himma da zage damtse wajen ganin sun kyautata alaƙarsu da mahaliccinsu a watan Ramadan, amma da zarar watan ya wuce sai kaga sun koma gidan jiya, wasu su koma aikin ɓarna, wasu kuma su tsaya da aikata aikin alkahairan da s**a kasance suna aikata a Ramadan.
Annabi (S.A.W.) ya kasance yana koyar da sahabbansa tabbata da tsayuwa tsayin daka akan aikin alkhairi. Ya tabbata a hadisi, watarana Sufyan ibn Abdullah Assaƙafiy ya tambayi Annabi (S.A.W.) ya faɗa masa wani abu wanda zai zama ya tattara komai a sha'anin addini ta yadda ba zai ƙara tambayar wani bayan manzon Allah ba, sai Annabi (S.A.W.) ya ce masa: "Kayi imani da Allah, sannan ka dai-dai ta".
Abdullahi ibn Abbas (R.A.) ya kasance yana fassara faɗin Allah (S.W.T.) acikin Suratul Fussilãt (30).
إن الذين الذين قالوا ربنا الله ثم استقاموا تتنزل عليهم الملائكة ألا تخافوا ولا تحزنوا وأبشروا بالجنة التي كنتم توعدون.()
Cewa Ma'anar ayar, s**a tsaya tsayin daka wajen yiwa Allah biyayya.
Alhasan -Allah yai masa rahama - ya kasance duk lokacin daya karanta ayar yana kance:
"اللهم فأنت ربنا فارزقنا الاستقامة"
Ya kasance daga cikin addu'oin Annabi (S.A.W.) k**ar yadda Imam Attairmithi, da Nasa'i s**a fitar:
"اللهم إني أسألك الثبات في الأمر ، والعزيمة على الرشد"
Dan haka yana daga cikin muhimmin abu maida hankali wajen aikin alkhairi bayan Ramadan, tare da dagewa da roƙon Allah akan ya tabbatar damu akan hakan, k**ar yadda aka samu magabata suna aikatawa.
Zulyadaini Auwal Abdullahi
3/Shawwal/1445H