07/08/2024
An fitar da jadawalin yadda Al'ummar Nigeria Zasu Dawo da Sanatocinsu da Yan Majilisu. Gasu kamar Haka...
Hanyoyi 9 da zaku bi wajen dawo da sanata ko dan majalisar da yake wakiltarku a Majalisa, idan zanga-zanga ta gagara, ku bi wannan hanyoyin don yin kiranye. Kafin ka karanta ka taimaka wajen yadawa zuwa waje 3 masu amfani don sakon yakaiwa ƴan Najeriya.
Ga matakan da za a bi domin kiran Sanatoci ko wakilai zuwa gida bisa rashin gansuwa da su da bakuyi ba a majalisa
1. Gano wakilan ku: Ku gano su wanene Sanatoci da wakilan ku a Majalisar Dokoki ta Kasa.
2. A cikin takardar zaku rubuta dalilin da yasa kuke son kiran wakilin ku dake majalisa.
3. Zaku rubuta bayanai dake cikin kundin tsarin mulkin kasa (Sashe na 69) na da Dokar Zabe.
4.zaku mika takardar koke ga hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) tare da bayyana dalilan kiranyen.
5. Zaku nemi goyon bayan mutane kashi 50% na waɗanda s**a yi rajista a mazabar wakilin.
6. Ko wsnnenku zai rubuta sa hannunsa a takardar da aka sanya wa hannu don mikawa hukumar zaɓe ta INEC.
7. Bayan kun kai hukumar zaɓe zata duba kwafin katin zabenku shin ya tabbata daga mazabar dan majalisar kuke ko Sanatan.
8. Idan an cika buƙatun sa hannu, za a gudanar da ƙuri'ar raba gardama don sanin ko za a sake kiran wakilin. Wannan kuma majalisa ce zata gudanar da shi.
9. Shiga cikin kuri'ar raba gardama kuma a karfafa wasu su yi haka.
An bayyana tsarin a sashe na 69 na kundin tsarin mulkin Najeriya da kuma dokar zabe. yana da mahimmanci a tuntuɓi masana shari'a da jami'an INEC don tabbatar da bin tsarin yadda ya kamata.
Don girman Allah mu yaɗa wannan Rubutu don ƴan uwan mu su amfana su bi don tabbatar da jagoranci nagari a Najeriya. Rubutawa :