29/04/2024
MALAMI DA DALIBINSA: PROF SALISU SHEHU & ABDULLAHI LAMIDO
Jiya nai kasida don nsa kare sunna
Bisa kan Tamalmatu wacce anka yi karya
Mai shekarunta dubu bakwai don shirme
Na fatattake su na wargaza musu karya
Sai Malamina Shehu yai yi kasidu
Yai jinjina ya fito ya goyan baya
Ga nan abinda ya ce cikin wakenai
In ka karanta sai ka bi ni a baya
"Allahu Akbar Allah kara basira,
Lamido ka zama Sha'iri fa na gaskiya
Abdallah tabbas ka cira mana tuta,
A wajen ginin shi'ri fa sam tankiya.
Kullum ka kan shiryo kasida qayyima,
Don kare Islama tafarkin gaskiya."
Babban liman ya karfafa mini baya
Masani na Ku'ani da ma tarbiyya
Bayan da nag na abinda Shehu ya tsaro
Ni ga abinda na ce ina godiyya
"Duk ƙoƙarin da muke a harkar da'awa
Ai ku ku kai mana dukkanin tarbiyya
Kuka bamu horo don mu k**a karatu
Ilimi da ƙwazo duk a gunku na koya
Ɗa ba shi yin kirki ya yo albarka
Sai in iyaye sun yi mar tarbiyya
Ku kun ce ma tsaya bisa Tauhidi
Mu rike kitabu mu ƙyale hanyar ƙaarya
Kuka sa mu ƙyam mu riƙe tafarkin Sunna
Mu guje wa musu ko yawan jayayya
Duk duniya ta san fa ni Abdallah
Ai Shaihunai ne sun ka sa ni a hanya
Kuma ko ina ne zam faɗi ba shakka
Kuma za ni nanata da babbar murya
Cewa a gunku na samu duk horona
Na zubo rubutu har da yin ƙafiyya
Roƙon Ilahu nake ya kare min ku
Ya tsare mu ranar lahira jin kunya
Ya saka mu firdausinsa mu da Habibu
Mu haɗe mu taru a can cikin soyayya"