Meye Lefina

Meye Lefina Kano

21/12/2024
A ranar 26 ga Janairu, 2006, a ka gano Joyce Carol Vincent a gidanta na Landan, ta zama kwarangwal, bayan ta mutu fiye d...
23/07/2023

A ranar 26 ga Janairu, 2006, a ka gano Joyce Carol Vincent a gidanta na Landan, ta zama kwarangwal, bayan ta mutu fiye da shekaru biyu a lokacin da ta ke kallon talabijin, wacce a ka samu a kunne ta na aiki har lokacin. Ta mutu a cikin Disamba 2003, ta mutu sak**akon cutar asma a yayin kallon talabijin.

08/06/2023

Idan banza ya maka aikin banza, kada kai ma ka zama banza ka tsaya rama aikin banza, yafi kyau kawai ka yi banza da banza.
©Anas Darazo

22/08/2022

ABOKINA MATASHI

Idan wani ya ce ka FIYE NEMAN KUƊI, don kana neman rufawa kanka asiri; ka lissafa masa expenses na kwana ɗaya (3 meals, cleansing kits, trans, subs...), ka ce za ka zauna a gida, ya biya ma buƙatunka na kwana ɗaya ma kawai.

Abokina!

Ka tashi ka nemi sana'a, za a ce ma,

"ka fiye naci"
"kana jin jiki, shi ya sa ka k**a sana'a"
"gari ne ya fara ma zafi"
"ka dage da neman kuɗi..oh"

Ka rubuta ka ajiye, masu yi ma waɗannan maganganun kashe gwuiwa, idan ka kafu, sune masu zuwa karɓar bashi, ko neman taimako.

Abokina!

Gaskiya magana, ba wani mai taimakonka, THIS LIFE IS 100% YOUR RESPONSIBILTY, KAI ZA KA TAIMAKI KANKA. Don ka yiwa (wani) ɗan siyasa campaing, ba ya nufin sai ya nema aiki. Project ne na campaing, kuma an baka kuɗin data (a lissafin ƴan siyasa).

Don uncle yana Director a Abuja, ko wani babban yaya na kasuwa, babu mai haƙƙi na dolen-dole sai ya baka kuɗi ko aiki, KYAUTATAWA IN SUN YI NIYYA. Ka fara taimakon kanka, tukun SAI SU TALLAFA MA.

Abokina!

In baka da sisi, ko sadaka ake nema a cikin masallaci, sai dai a wuce da akwatin Fisabilillah ta gabanka kana susar kai, baka iya sa hannu a aljihu.

Manufar sana'a ita ce, samun kuɗin rufa kai asiri, biyawa kai bukatu na dole (abin ci, muhalli, lafiya, ilimi, sutura...), nesanta kai daga wofantar da daga roko ko dogara da wani. Ba wai a tara 'luxuries" aka taƙama da fank**a ba.

Waɗannan manyan motoci, da danƙareran gida, da manyan rigunan da kake sha'awa, kafin a same su, sai da aka yi gumi, aka sha gwargwarmaya. Kai ma ka tashi ka nema, Allah zai baka fiye da wannan in Ya ƙaddara. Ba mai ɗaukar ƴarsa ya ba ka, ba ka da kuɗi, ba ka da sana'a.

20/08/2022

An buɗe shafin BBC Hausa Facebook ne ranar 4 ga watan Agustan 2009 don wallafa labarai da bidiyo a harshen Hausa.

Address

Gwale Lcl Gvrnmt
Kano
KANO

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Meye Lefina posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Business

Send a message to Meye Lefina:

Share