UMG Tech solutions

UMG Tech solutions Contact information, map and directions, contact form, opening hours, services, ratings, photos, videos and announcements from UMG Tech solutions, Financial Consultant, Office No. 5 Kaita House, along Yahaya Madawaki Way, Kofar Kaura Katsina, Katsina.

UMG Tech solutions specialized on web design and development, media and graphics design, computer training, we provide these services to corporate, government, students, individuals and international donor clients.

Gwamnatin Tarayya Ta Ayyaɗa Ranakun Alhamis Da Juma'a A Matsayin Hutu Domin Bikin Babbar SallahGwamnatin Tarayya ta ayya...
17/03/2026

Gwamnatin Tarayya Ta Ayyaɗa Ranakun Alhamis Da Juma'a A Matsayin Hutu Domin Bikin Babbar Sallah

Gwamnatin Tarayya ta ayyana ranakun Alhamis, 19 ga Maris, da Juma’a, 20 ga Maris, 2026 a matsayin ranakun hutu na ƙasa domin bikin Eid-el-Fitr, wanda ke nuna ƙarshen azumin watan Ramadan.

Ministan Harkokin Cikin Gida, Olubunmi Tunji-Ojo, ne ya sanar da hakan a madadin Gwamnatin Tarayya, ta cikin wata sanarwa da Babbar Sakatariyar ma’aikatar, Magdalene Ajani, ta fitar a ranar Talata.

A cikin sanarwar, ministan ya taya al’ummar Musulmi murnar kammala azumin Ramadan lafiya, tare da kira gare su da su ci gaba da riƙo da kyawawan ɗabi’u da aka koya a watan mai alfarma, kamar ƙauna, haƙuri, sadaukarwa, zaman lafiya da kuma taimakon juna.

Hakazalika, ya buƙaci ‘yan Najeriya da su yi amfani da wannan lokaci wajen yin addu’o’i domin zaman lafiya, haɗin kai da ci gaban ƙasa baki ɗaya.

Gwamnatin ta kuma shawarci al’umma da su gudanar da bukukuwan cikin natsuwa da lumana, tare da miƙa hannu ga marasa galihu domin su ma su ji daɗin bikin.

Gwamnatin Tarayya ta sake jaddada aniyarta na ƙarfafa haɗin kan ƙasa da zaman lafiya tsakanin dukkanin al’ummomin Najeriya.

Yaya kuke shirin gudanar da bikin Eid-el-Fitr bana? Kuma wane irin mataki kuke ganin ya kamata mu ɗauka domin tallafa wa marasa ƙarfi acikinmu a wannan lokaci?

Tarihi a Hoto: Fitattun Jagororin Kano Uku a Wani Tsohon LokaciWani hoto na musamman daga shekarun 1960 ya sake jawo han...
17/03/2026

Tarihi a Hoto: Fitattun Jagororin Kano Uku a Wani Tsohon Lokaci

Wani hoto na musamman daga shekarun 1960 ya sake jawo hankalin jama’a, inda ya haɗa manyan mutane uku da s**a taka rawa a tarihin Arewacin Najeriya—marigayi Sarkin Kano Ado Bayero, marigayi Galadiman Kano Tijjani Hashim, da kuma fitaccen ɗan kasuwa Aminu Dantata—a lokacin ƙuruciyarsu.

An sake bayyana hoton a shafukan sada zumunta a ranar 15 ga Yuli, 2024, inda a wancan lokaci aka nuna cewa Aminu Dantata ne kaɗai ke raye daga cikin su. Sai dai bayan shekara guda kacal, ya rasu a ranar 28 ga Yuni, 2025, lamarin da ya sanya hoton ya zama wata shaida ta tarihi mai ɗauke da darasi kan sauyin zamani.

A rayuwarsa, Aminu Dantata ya kasance ginshiƙi a fannin kasuwanci da ayyukan jin ƙai, inda ya taɓa rike muƙamin Kwamishinan Raya Tattalin Arziki, Kasuwanci da Masana’antu na Jihar Kano a ƙarshen shekarun 1960. Haka kuma, shi ne kawun attajirin duniya Aliko Dangote, wanda ya gaji irin wannan hangen nesa a harkar kasuwanci.

Masana na ganin irin waɗannan hotuna na tarihi na taimakawa wajen tuna irin gudunmawar da tsofaffin shugabanni s**a bayar, tare da haskaka yadda jagoranci, kasuwanci da sarauta s**a haɗu wajen gina al'umma.

A ra’ayinku, shin shugabannin wannan zamani na koyo daga irin jagoranci da gudunmawar da waɗannan dattawa s**a bayar, ko kuwa akwai gibi da ya kamata a cike, sannan wani irin darasi kasamu a cikin tarihin magabatan arewa?

Innalillahi Wa Inna Ilaihir Raji’un: Harin ‘Yan Bindiga Ya Hallaka Mutane 15 a KatsinaA wani mummunan lamari da ya girgi...
17/03/2026

Innalillahi Wa Inna Ilaihir Raji’un: Harin ‘Yan Bindiga Ya Hallaka Mutane 15 a Katsina

A wani mummunan lamari da ya girgiza al’umma, akalla mutane 15 ne s**a rasa rayukansu sakamakon arangama tsakanin ‘yan bindiga da masu gadin gari da ‘yan sa-kai a ƙauyen Falele, gundumar Daddara, ƙaramar hukumar Jibia a Jihar Katsina.

Rahotanni sun nuna cewa harin ya faru ne da misalin ƙarfe 1:30 na rana, lokacin da ‘yan bindiga s**a kai farmaki cikin gari, lamarin da ya haddasa musayar wuta mai tsanani tsakaninsu da jami’an tsaron al’umma.

Kwamishinan Tsaro da Harkokin Cikin Gida na jihar, Nasir Mua’zu, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya bayyana cewa rikicin ya shafi ƙauyukan Falele da Kadobe. Ya ce jami’an tsaro sun samu nasarar dawo da zaman lafiya bayan an yi asarar rayuka 15.

A cewarsa, ‘yan sa-kai sun fafata da wasu tubabbun ‘yan bindiga, inda aka samu asarar rayuka uku daga cikinsu, lamarin da ya haifar da wani harin ramuwar gayya wanda ya ƙara tsananta asarar rayuka a yankin.

Jami’an tsaro daga rundunar ‘yan sanda, DSS, Civilian Watch (C-Watch), tare da shugabannin al’umma sun haɗa kai wajen shawo kan lamarin, tare da dakile cigaba da tashin hankali.

Sai dai duk da wannan mataki, al’umma na ci gaba da nuna matuƙar damuwa kan yadda hare-hare ke faruwa ko da a tsakar rana, abin da ke nuna tsananin ƙalubalen tsaro a yankin.

Rahotanni daga mazauna yankin sun bayyana cewa waɗanda aka kashe ba su da wani laifi, kuma wasu daga cikinsu na cikin azumi a lokacin da aka kai harin, abin da ya ƙara jawo alhini da jimami a zukatan jama’a.

Shin har yaushe za mu ci gaba da zama cikin wannan hali? Me ya kamata mu a matsayin al’umma mu fara yi kai tsaye domin kare kanmu, haɗa kai, da hana ‘yan ta’adda ci gaba da addabar rayukanmu?

Shin lokaci bai yi da za mu ƙarfafa tsaron al’umma, mu daina shiru, mu hada kanmu domin ganin an kawo karshen wannan ta'addanci dake kara yawa akoda yaushe?

17/03/2026

Zancen Zuciya ❤️ Part 1

A shirin yau, Amira Fine Girl ma ta ƙi amincewa da tayin Malam Abdulhakim, inda ta bayyana mashi tana da saurayin da takeso. Lamarin ya tayar da muhawara—shin ko Amira zata ba Malam Dama ya akan ya jaraba sa'arshi koko zata zabi tsohuwar zuma?

Kai fa ko ke fa, meye kake ko k**e fara dubawa a kafin kaba mutum damar ya shiga rayuwarka?

09/03/2026

Har makaho nayi ma jagora domin a rufa ma kai asiri - GM Mahuta

Peter Obi Ya Sabunta Rajistarsa na jam'iya a African Democratic Congress (ADC)Tsohon dan takarar shugaban kasa, Peter Ob...
08/03/2026

Peter Obi Ya Sabunta Rajistarsa na jam'iya a African Democratic Congress (ADC)

Tsohon dan takarar shugaban kasa, Peter Obi, ya kammala sabunta rajistar mambobinsa a jam’iyyar African Democratic Congress (ADC), yana mai kira ga jam’iyyun adawa da su hada kai domin kawo karshen mummunan shugabanci a Najeriya.

Obi ya bayyana hakan ne bayan wani babban taro da aka gudanar a Awka, inda aka kaddamar da shirin tantancewa da rajistar mambobin jam’iyyar. Taron ya samu halartar sanatoci biyu, mambobin majalisar tarayya biyar da kuma ‘yan majalisun dokokin jiha shida tare da wasu manyan baki.

Ya kuma tuna da wani taro da aka yi a ranar 31 ga Disamba a Enugu, inda manyan shugabannin yankin Kudu maso Gabas s**a hadu domin kira ga ‘yan siyasa da masu ruwa da tsaki su rungumi jam’iyyar ADC a matsayin dandalin kawo sauyi a siyasar Najeriya.

Daga cikin manyan shugabannin da s**a halarci taron akwai Okwesilieze Nwodo, Emeka Ihedioha, Achike Udenwa, Enyinnaya Abaribe, da Victor Umeh, da sauran manyan ‘yan siyasa daga yankin.

Bayan kaddamar da shirin a Awka, Obi ya wuce zuwa Agulu, inda ya kammala sabunta rajistarsa a matsayin mamba na jam’iyyar tare da karfafa gwiwar magoya baya su shiga cikin harkokin siyasa domin samar da sauyi.

Ya jaddada cewa zaben shekarar 2027 ba zai kasance kawai fafatawa tsakanin jam’iyyun siyasa ba, sai dai zabi ne tsakanin al’ummar Najeriya da kuma mummunan shugabanci.

Bola Ahmed Tinubu Ya Amince da Karin Albashin Sojojin NajeriyaShugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya amince da karin albas...
08/03/2026

Bola Ahmed Tinubu Ya Amince da Karin Albashin Sojojin Najeriya

Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya amince da karin albashi ga jami’an Nigerian Armed Forces domin inganta jin dadin su da kuma kara musu kwarin gwiwa wajen gudanar da ayyukansu na kare kasa.

Matakin na daga cikin kokarin gwamnatin tarayya na inganta walwalar jami’an tsaro, musamman a lokacin da suke ci gaba da fuskantar kalubalen tsaro a sassa daban-daban na Najeriya.

Ana sa ran karin albashin zai kara karfafa gwiwar sojoji tare da inganta aikin tsaro da suke yi domin tabbatar da zaman lafiya da tsaron rayuka da dukiyoyin al’umma.

Gwamnatin Jihar Katsina Ta Amince Da Sayo Babura 3,000 Masu Amfani da Wutar Lantarki Domin Taimaka wa Malaman KarkaraGwa...
08/03/2026

Gwamnatin Jihar Katsina Ta Amince Da Sayo Babura 3,000 Masu Amfani da Wutar Lantarki Domin Taimaka wa Malaman Karkara

Gwamnatin Jihar Katsina karkashin jagorancin Gwamna Dikko Umaru Radda ta amince da sayen babura 3,000 masu amfani da wutar lantarki (Electric Motorbikes) domin rabawa ma’aikata, musamman malamai da ke koyarwa a kauyuka da yankunan da ke da nisa.

Matakin ya biyo bayan koken da malamai s**a dade suna yi kan matsalar sufuri da wahalar zuwa makarantu a yankunan karkara. Gwamnan ya saurari koken tare da daukar matakin gaggawa domin samar da wannan tallafi.

Ana sa ran shirin zai taimaka wajen saukaka zirga-zirgar malamai zuwa wuraren aiki, rage musu nauyin kudin sufuri da kuma inganta aikin koyarwa a makarantu.

Masana ilimi na ganin cewa tallafa wa malamai wajen saukaka zuwa makaranta na daga cikin muhimman matakan da za su taimaka wajen bunkasa harkar ilimi a jihar.

Gwamnatin Tarayya Ta Amince da Karin Gurabe 50,000 Ga Shirin NYSC na 2026Gwamnatin Tarayya ta amince da karin gurabe 50,...
08/03/2026

Gwamnatin Tarayya Ta Amince da Karin Gurabe 50,000 Ga Shirin NYSC na 2026

Gwamnatin Tarayya ta amince da karin gurabe 50,000 domin shirin National Youth Service Corps (NYSC) na shekarar 2026.

Matakin ya biyo bayan karuwar yawan daliban da s**a kammala karatu a jami’o’i da sauran manyan makarantu, wadanda ke jiran shiga shirin bautar kasa.

Ana sa ran karin guraben zai taimaka wajen rage cunkoson masu jiran shiga shirin NYSC, tare da ba karin matasa damar gudanar da hidimar kasa cikin lokaci.

🕋 SPONSORED POST — UMG TRAVEL & TOURS✈️ Cheap and Best Umrah Package in NigeriaPrepare for Shawwal Umrah 2026 with comfo...
07/03/2026

🕋 SPONSORED POST — UMG TRAVEL & TOURS

✈️ Cheap and Best Umrah Package in Nigeria

Prepare for Shawwal Umrah 2026 with comfort and peace of mind. Travel with ease, worship with focus, and let UMG Travel & Tours handle every detail of your journey.

📅 Departure Date: 24 March 2026

💼 Package Includes:
• Umrah Travel Visa
• Flight Ticket
• Hotel / Accommodation
• Free Local Transportation
• Professional Umrah Guide
• 24/7 Support Throughout Your Journey

💰 Discount Price: ₦2.3 Million Only

📞 Call or Whatsapp: 08081432912,07061911120

📍 Office Address:Along Secretariat Road, Behind Barhim Estate, Katsina.

Email: [email protected]

Travel with peace. Worship with ease.
Let UMG Travel & Tours take care of your Umrah journey.

07/03/2026

Address

Office No. 5 Kaita House, Along Yahaya Madawaki Way, Kofar Kaura Katsina
Katsina
234

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when UMG Tech solutions posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Business

Send a message to UMG Tech solutions:

Share