21/07/2023
Karanta labarin mutumin da a yanzun haka ya share shekaru 60 ba tare da ya taba ko gyangyadawa ba balanta ya yi barci
Daga Wakiliya
Wannan shine Thai Ngoc mutumin da akace tsawon shekara 60 bai taba yin barci ba, yanzu shekararsa 80 a duniya, dan kasar Vietnam an haife shi a 1942.
Duk binciken da masana s**ayi akansa basu gane dalilin rashin wannan barci na Mista Thai Ngoc ba.
Wakiliya ta gano an sha samun yan jarida da masu bincike suna zuwa kauyen Mista Thai Ngoc su kwana dashi domin tabbatar da ikirarin dayake yi amma haka zasu zauna har washe gari ko gyangyadi baya iya yi.
An sha fama da Ngoc ya bari a kaishi manyan cibiyoyin bincike domin ayi masa gwaje-gwaje amma yaki yarda domin yana tsoron asibiti
Mai karatu kaima kana iya yin naka binciken akan labarin wannan mutumi....