05/09/2025
Munyi Mauludin Annabi SAW A Green House.
Mukasance mu kwaikwayi Gaskiya da Rikon Amana, cikin dabiun fiyayyen Halitta, zamuci Nasara a rayuwarmu, inji shugaban Kamfanin Alh shehu Sani Namaska Green House Katsina, a takardar sakon sa da Isah sani yakaranta,
Angudanar da Mauludin yau da misalin 7:00am zuwa 8:30am yau 12 ga watan rabiul awwal Wanda yai daidai da 5/9/2025, angudanar da Mauludin a harabar Kamfanin da ake ma lakabi da Green House complex.
Bayan gabatar da karatun Qur'ani manajan company Alh Salisu shehu, yayi Bayanin kan makasudin wannnan taro shine, taruwa mu nuna godiya ga Allah da yabamu Fiyayyen Halitta Annabi Muhammad SAW daga bisani aka gudanar karatun da Diwani gami da Ishirinya. Bayan Kara Kara tun Al'qurani.
Director na company Alh Sani shehu ne yayi jawabin rufewa, inda yayi kira akan mukasance masu hakuri saboda hakuri haline na Manzon Rahama SAWW sannan da hakuri zamu iya nasara akasuwancinmu.
Daga karshe M Didi ya rufe da addua.