25/06/2023
Bola Ahmed Tinubu ya sa hannu a kudirin kare bayanai, tuni ta zama doka da za tayi aiki a NajeriyaShugaban kasar ya yi alkawarin yin hanyar da mutum miliyan 1 za su samu aiki a wannan bangareWannan mataki da Tinubu ya dauka zai yi sanadiyyar da kusan mutum 500, 000 za su samu na abinci
Abuja - A farkon makon ne Mai girma Bola Ahmed Tinubu ya sa hannu a kudirin kare bayanai wanda tuni ta zama doka mai aiki a Najeriya.
Kamar yadda rahoto ya fito dagaLeadership, kimanin mutane 500, 000 ake sa ran za su amfana da wannandoka, su samu ayyukan yi a kasar nan.
Hanyoyin da dokar za ta rage marasa aikin yi sun hada da horas da jami’an kare bayanai da bada lasisi ga kamfanonin tabbatar da bin doka.
Kara karanta wannan
Wata Sabuwa: Fastoci Sun Waigo Ga Tinubu da Wasu Bukatu, Sun Ce Dole ya Cika Musu Alkawari
Shugaban kasa, Bola Tinubu a fadarsa Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu Asali: Facebook
Wadannan kamfanonin da za a kafa, za su yi aiki da masu kula da bayanai da masu sarrafa shi.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Rattaba hannu a kan kudirin har ya zama doka ya na daga cikin alkawuran da Bola Ahmed Tinubu ya yi wa jama’a a lokacin da yake neman zabe.
Alkawari ya cika
Da yake neman zama shugaban kasa, Bola Tinubu ya sha alwashin magance zaman kashe wando, ya ce zai samar da ayyuka miliyan daya a fannin.
Tattalin arziki na zamani ya na cikin fannonin da matasa za su iya shiga domin neman arziki.
Jami'an NDPM sun yi karin haske
Babban jami’in bangaren tabbatar da shari’a da bin dokoki na NDPB, Babatunde Bamigboye, ya fitar da jawabi ya na mai wannan bayani a jiya.
A cewar wani babban kwamishina a NDPB, Dr. Vincent Olatunji dokar da aka shigo da ita za ta tabbatar da ‘yancin ‘yan kasa a kafar yanar gizo.
Kara karanta wannan
Wasa farin girki: Yadda tun farko Tinubu ya hango Emefiele na masa tuggu a zaben 2023
Baya ga samun ‘yanci, dokar za ta kare sirrin masu yin cefane ta kafafen yanar gizo na zamani.