18/07/2025
Shin kai ma'aikaci ne aiki ya yi maka yawa a ofis, amma kana da sha'awar iya karatun Alƙur'ani, ko kai ɗan kasuwa ne harkokin kasuwanci sun yi maka yawa, amma zuciyarka na fatan ta iya Alƙur'ani, ko kuma ka riga ka ajiye aiki, amma kana da son Alƙur'ani?
Shin kana da yara da kake so su iya Alƙur'ani, amma yanayin zama a kudancin Nijeriya ko kuma a ƙasashen waje, bai baka damar cimma burinka ba na sama masu cikakkiyar damar koyon Alƙur'ani?
Abokai ne ku, ko kuwa ƙungiya ce, amma Allah Ya saka maku son iya littafin Allah?
Kana da iyali da ke son iya littafin Allah?
To ku zo ku ji, DigiScholars Consulting ta samar maku mafita akan wannan mafarki naku na iya fiyayyen littafi a ban ƙasa, watau Alƙur'ani.
Mun shirya tsaf, a harshen da kuke so, da kuma lokacin da kuke so a sanya maku don koyon littafin Allah.