KUMO TV

KUMO TV Barka Da Zuwa;

Ku Cigaba Da Kasancewa Da Kumo Tv Mai Tsage Gaskiya Komai Dacin ta, Ba Ta

LABARI MAI DADI YANZU-YANZU: Kamfanin ABBA PANTAMI DATA LTD, ya rage muku farashin Data, kowa ya duba Application dinshi...
19/10/2025

LABARI MAI DADI

YANZU-YANZU: Kamfanin ABBA PANTAMI DATA LTD, ya rage muku farashin Data, kowa ya duba Application dinshi domin more garabasa.

Sako Zuƙowa GaMai Girma Gwamnan Jihar GombeRt. Hon. Kakakin Majalisar Dokokin Jihar GombeHon. Shugaban Karamar Hukumar A...
06/10/2025

Sako Zuƙowa Ga

Mai Girma Gwamnan Jihar Gombe

Rt. Hon. Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Gombe

Hon. Shugaban Karamar Hukumar Akko

Senatan. Gombe ta tsakiya

Rt. Hon. Majalisar Dokokin Tarayya

Batun- Buƙatar Shigar da Garin Alkali, Garin Liman da jauro Musa kumo cikin Ayyukan Ci gaba

Da farko, mu al’ummar Garin Alkali, Garin Liman da jauro Musa muna miƙa godiya ga Allah Maɗaukaki, sannan kuma muna mika godiya da yabo gareku shugabanni bisa irin ƙoƙari da jajircewa wajen kawo ayyukan ci gaba a yankinmu na Garin Kumo da kewaye.

Duk da irin wannan cigaba, muna mai sanar da ku cewa, al’ummar Garin Alkali, Garin Liman da jauro Musa duk da kasancewarsu masu bada gudummawa mai yawa a lokutan zaɓe sun dade suna kasancewa a baya wajen cin gajiyar romon dimokuraɗiyya. Wannan ya shafi fannoni da dama musamman:

1. Ayyukan Tituna: Muna buƙatar a haɗa mu cikin shirin gina tituna da ake aiwatarwa a Garin Kumo domin rage wahalhalun zirga-zirga da matsalolin sufuri.

2. Wutar Solar: A tabbatar da saka hasken wutar solar a unguwanninmu domin kawo ƙarshen duhu da matsalar rashin wuta.

3. Matsalar Zaizayar Ƙasa: Garin Liman da jauro Musa ya dade suna fama da matsalar zaizayar ƙasa wadda ke barazana ga al’umma, duk kuwa da roƙon da aka ta gabatar tun shekaru da dama da s**a wuce.

Mun yi imanin cewa, idan aka kula da waɗannan bukatu, zai taimaka wajen rage matsalolin yau da kullum da al’ummarmu ke fuskanta, tare da ƙara haɗa su cikin tsarin ci gaban jihar.

Saboda haka, muna kira ga shugabannin siyasa na wannan yanki, tare da matasa da s**a shiga harkar siyasa, da su ɗauki koken al’ummarmu, domin a tabbatar da cewa Garin Alkali, Garin Liman da jauro Musa sun ci gajiyar dimokuraɗiyya kamar sauran yankuna.

Allah ya sanya wannan sako ya isa inda ake so, ya kuma sa ku sami nasara da albarka a dukkan ayyukan alheri.

✍️Muhammad chigari kumo
(Chigarin Barunde)
Madadin Al’ummar Garin Alkali, Garin Liman da Jauro Musa kumo

Kira ga Gwamnati da Masu Ruwa da TsakiDuba da yadda al’ummar Garin Alkali da Garin Liman suke taka muhimmiyar rawa wajen...
03/10/2025

Kira ga Gwamnati da Masu Ruwa da Tsaki

Duba da yadda al’ummar Garin Alkali da Garin Liman suke taka muhimmiyar rawa wajen bayar da gudummawa a lokacin zaɓe, ya dace a tabbatar da cewa suma sun amfana daga ayyukan ci gaba da ake aiwatarwa a Garin Kumo. Ayyuka irin su gina tituna da kuma saka wutar Solar ya kamata su kai har zuwa waɗannan yankuna, domin su ma su ci gajiyar romon dimokuraɗiyya.

Yankunan Garin Alkali da Garin Liman sun daɗe suna kasancewa a bayan baya wajen samun albarkacin ci gaban Gwamnati duk da yawan jama’ar da ke zaune a wuraren. Musamman ma Garin Liman ya shafe lokaci mai tsawo yana fama da matsalar zaizayar ƙasa, wacce ta addabi al’umma har zuwa yau.

Saboda haka, muna kira ga manyan ‘yan siyasa na wannan yanki tare da matasa masu tasowa a harkokin siyasa da su riƙa ɗaukar koken al’ummomin nan, domin a shigar da su cikin tsarin samun ci gaba.

Mu na roƙon Allah Madaukakin Sarki Ya sanya wannan kira ya isa inda ake so, kuma ya zamo abin amfana ga al’ummarmu baki ɗaya.

Daga Muhammad chigari kumo

2nd October,2025 Tawagar Yahaya Barambu   ta marabci Uwar Gidan Shugaban Ƙasar Najeriya, Sen. Oluremi Bola Ahmed TinubuD...
02/10/2025

2nd October,2025

Tawagar Yahaya Barambu ta marabci Uwar Gidan Shugaban Ƙasar Najeriya, Sen. Oluremi Bola Ahmed Tinubu

Da safiyar yau Alhamis, 02/10/2025, tawagar Bldr. Yahaya Yahaya Barambu ta gudanar da kyakkyawar maraba ga Uwar Gidan Shugaban Ƙasar Najeriya, Sanata Oluremi Bola Ahmed Tinubu, a garin Kumo, hedkwatar Ƙaramar Hukumar Akko.

Tawagar mai ƙarfin gaske ta fito fili da nuna bajinta, basira, hikima da ƙwarewa ƙarƙashin jagorancin jajirtaccen matashin ɗan siyasa, Hon. Safiyanu Danladi Mairiga (Sadaukin Gona), Mataimaki na Musamman ga Mai Girma Gwamnan Jihar Gombe, His Excellency Alh. Muhammadu Inuwa Yahaya, CON (Ɗan Majen Gombe) akan harkokin Kafofin Sadarwa.

Taron ya samu halartar Mai Girma Gwamnan Jihar Gombe tare da manyan masu ruwa da tsaki daga cikin jihar da kuma daga sassa daban-daban na ƙasar.




📸 Auwal Labaran AAuwal Labaran Shehu

Behold the Sarauniya Yakin Kumo - the Queen Warrior of Akko Emirate, It is indeed an honour to be so recognized.— Senato...
02/10/2025

Behold the Sarauniya Yakin Kumo - the Queen Warrior of Akko Emirate, It is indeed an honour to be so recognized.

— Senator Oluremi Tinubu, CON

NEMAN TAIMAKO! NEMAN TAIMAKO!‘Yan uwa da abokan arziki, muna neman taimakon ku a wannan lokaci mai muhimmanci.Wannan tak...
29/09/2025

NEMAN TAIMAKO! NEMAN TAIMAKO!

‘Yan uwa da abokan arziki, muna neman taimakon ku a wannan lokaci mai muhimmanci.

Wannan takaddar gwaji da kuke gani ta Goggo Addayo Dakkiti, wadda aka yi mata scanning tun ranar 16/09/2024. Likitoci sun tabbatar da cewa tana bukatar Lumbosacral Surgery, amma kudin aikin ya gagara saboda halin rayuwa.

Tun kimanin shekaru uku, Goggo tana fama da jinya mai tsanani, inda komai sai an mata, kuma yanzu haka tana kwance a gida cikin wahala

Duk wani mai jinya yasan cewa, jinya mai ɗaukar lokaci tana cin ƙarfi da ƙimarsa, b***e wadda ta kai tsawon shekaru.

A halin yanzu, ana buƙatar Naira Dubu Dari Takwas (₦800,000) domin gudanar da wannan aikin tiyata tare da sauran dawainiyarsa.

Saboda haka, muna roƙon ‘yan uwa Musulmai da masu zuciya ta alheri, kusa da nesa, da su taimaka gwargwadon iko ko da sisi ne, ko kuma daukar nauyin gaba ɗaya.
Idan ba da kai tsaye ba, zaka iya yada wannan saƙo zuwa kunnuwan wanda zai iya taimakawa.

Muna addu’a Allah ya ba Goggo lafiya, ya kuma ba kowane mara lafiya lafiya, ya kuma ƙara mana lafiya garemu da ‘ya’yanmu.

Ga lambobin tuntuɓa / bada gudunmawa:
09030772989
09039796363
08034829056

Dr. Bashir Abdullahi Gaddafi  Jagoran Al’umma, Ba Tare da Mukami BaA yau, Hon. Dr. Bashir Abdullahi Gaddafi ya sake tabb...
05/09/2025

Dr. Bashir Abdullahi Gaddafi Jagoran Al’umma, Ba Tare da Mukami Ba

A yau, Hon. Dr. Bashir Abdullahi Gaddafi ya sake tabbatar da cewa siyasa ba lallai ta tsaya kan mukami ba, illa hidima ga al’umma.

Ya bayar da Naira miliyan 1,500,000 (1.5m) domin gyaran Transformer na Anguwan Jerusalem, tare da ƙarin Naira dubu 800,000 domin gyaran Transformer na Anguwan Black Market.

Wannan ayyuka sun kara tabbatar da cewa Dr. Gaddafi shi ne jagoran da ya ke kula da jama’arsa ba tare da wani kujerar siyasa ba. A tarihi, babu wani ɗan siyasa a Akko da ya yi hidima irin ta Dr. Gaddafi tun kafin samun mukami.

Dr. Gaddafi nagartaccen shugaba ne, wanda burinsa shi ne ganin jama’arsa sun fita daga duhu zuwa haske, daga ƙunci zuwa jin daɗi.

Muna addu’a Allah ya kara masa iko, ya tsare shi, ya kuma bamu sa’a a siyasar 2027, domin samun shugaba nagari wanda al’umma ke alfahari da shi.

Yadda Aka Gudanar da Bikin Makon Ƙungiyar Ɗaliban Aikin Jarida (MACOSA Week) A Jami’ar Tarayya Kashere, Jihar GombeA jiy...
01/07/2025

Yadda Aka Gudanar da Bikin Makon Ƙungiyar Ɗaliban Aikin Jarida (MACOSA Week) A Jami’ar Tarayya Kashere, Jihar Gombe

A jiya Litinin, Ƙungiyar Ɗaliban Sashen Kimiyyar Yada Labarai ta Jami’ar Tarayya Kashere (MACOSA) ta kammala bikin makonta cikin wani gagarumin taron ilimi na musamman (symposium) da aka shirya domin faɗaɗa tunanin ɗalibai da mahalarta kan ci gaban fasaha da tasirinta a fannin aikin jarida.

Babban bako kuma mai jawabi na musamman (Keynote Speaker) a taron shi ne mai girma Shugaban Jami’ar Tarayya Kashere, Farfesa Umaru A. Pate mashahurin masanin kimiyyar yada labarai da ilimin sadarwa, wanda ya yi fice a Najeriya da ma duniya baki ɗaya.

Taken Taron:

Juyin Juya Halin Fasahar AI a Fannin Jarida: Muhimman Hanyoyin Kiyaye Ka’idoji da Mafi Kyawun Ayyuka.”

A cikin jawabinsa, Farfesa Pate ya yi bayani mai zurfi kan yadda fasahar wucin gadi (Artificial Intelligence - AI) ke sauya fasalin aikin jarida, daga matakin rubuce-rubuce zuwa tantancewa da rarraba labarai. Ya bayyana yadda AI ke kawo sauƙi da sauri wajen gudanar da aiki, amma a lokaci guda yana haifar da manyan ƙalubale dangane da sahihanci, amincewa, da kiyaye ka’idojin aikin jarida.

Ya jaddada bukatar ɗalibai da malamai su fahimci wannan sauyi a matsayin wata dama ta ci gaba, amma mai buƙatar ilimi, ƙwarewa da kiyaye ƙa’idodi. Har ila yau, ya nuna muhimmancin koyarwa da tsara manufofi masu inganci wajen amfani da fasahar AI, domin kare martaba da darajar aikin jarida.

Taron ya kasance mai cike da nishadi, ilmantarwa da tattaunawa mai zurfi tsakanin kwararru, malamai da ɗalibai, inda aka bayyana ra’ayoyi mabanbanta kan makomar aikin jarida a wannan zamani na dijital.

✍️ Muhammad Chigari Kumo

Arewa Media Writers Na Kira Ga Gwamnatin Tarayya Da Jihohin Filato Da Benue Kan Kisan Matasan ArewaDaga Arewa Media Writ...
25/06/2025

Arewa Media Writers Na Kira Ga Gwamnatin Tarayya Da Jihohin Filato Da Benue Kan Kisan Matasan Arewa

Daga Arewa Media Writers

Ƙungiyar marubutan Arewa a kafafen sada zumunta, Arewa Media Writers, ƙarƙashin jagorancin Comr Haidar H. Hasheem, ta bayyana damuwa da alhini game da kisan gillar da aka yi wa matasan Arewa a jihohin Filato da Benue a cikin makon nan, tare da kira ga gwamnati da hukumomin tsaro da su gaggauta ɗaukar mataki.

A cewar ƙungiyar, a jihar Benue, an kashe Barhama Suleiman da Jamilu Ahmad, matasa 'yan asalin jihar Kano, bayan da wasu da ake zargin ‘yan ta’adda ne s**a tare motarsu s**a hallaka su. An gudanar da jana'izarsu a babban masallacin ƙasa da ke Abuja, inda manyan jami'ai ciki har da Nuhu Ribadu da Gwamna Abba Kabir Yusuf s**a halarta.

Haka kuma, a jihar Filato, matafiya daga Zaria, yawancinsu ’yan asalin Basawa, sun rasa rayukansu yayin da suke kan hanyarsu ta zuwa bikin aure. Akalla mutum 12 ne s**a mutu a harin da aka kai a karamar hukumar Mangu.

Ƙungiyar ta bayyana cewa kisan gillar ba sabon abu ba ne, domin an dade ana kai wa 'yan Arewa hari a waɗannan yankuna, amma ba a ganin hukunci ko mataki daga hukumomi. Wannan shiru da sakaci na gwamnati yana ƙara nuna gazawar tsarin tsaro da rashin adalci ga ’yan Arewa.

Shin rayukan ‘yan Arewa ba su da ƙima? Ko kuwa gwamnati na da hannu a ciki ?

Arewa Media Writers ta yi kira ga Gwamnatin Tarayya da jihohin da abin ya shafa da su:

1. Gaggauta bincike da gurfanar da masu hannu a gaban kuliya.

2. Bayyana matsayi a fili kan kisan gillar da ake wa ‘yan Arewa.

3. Hukumomin tsaro (’Yan Sanda, DSS) su gudanar da bincike tare da bayyana sakamakon.

4. Majalisar dokoki ta kaddamar da bincike kai tsaye kan yawaitar kashe-kashen ’yan Arewa.

Ƙungiyar ta ƙara da cewa, irin wannan rashin adalci na barazana ga zaman lafiya da hadin kan Najeriya, don haka dole ne a tabbatar da cewa jinin ɗan Arewa yana da daraja kamar na kowa.

Idan gwamnati ba za ta kare rayukan ‘yan Arewa ba, mu da harshenmu da alkalumanmu za mu ci gaba da tashi tsaye har sai an yi mana adalci.







Rubutawa, Muhammad Kwairi Waziri, National Director Media And Publicity II Arewa Media Writers.

Duk Wanda ya sayi Datar 1GB ta MTN mai 30DAYS a cikin Application din ABBA PANTAMI DATA LTD, to sai tayi kwanaki 30 sann...
22/06/2025

Duk Wanda ya sayi Datar 1GB ta MTN mai 30DAYS a cikin Application din ABBA PANTAMI DATA LTD, to sai tayi kwanaki 30 sannan za tayi Expired

Barumde School Of Health Technology, Kumo Ta Yaye Rukunin  Dalibai Karo Na Uku.Daga. Adamu Muhammad Chigari Makarantar B...
03/05/2025

Barumde School Of Health Technology, Kumo Ta Yaye Rukunin Dalibai Karo Na Uku.

Daga. Adamu Muhammad Chigari

Makarantar Barumde School of Health Technology, Kumo, ta gudanar da bikin yaye daliban ta na bana, inda daruruwan dalibai daga sassa daban-daban s**a karɓi shaidar kammala karatu a fannoni daban-daban na kiwon lafiya.

Bikin wanda aka gudanar a harabar makarantar ya samu halartar manyan baki daga hukumomin lafiya, iyaye da 'yan uwa, da kuma al’ummar gari. A yayin taron, shugaban makarantar ya bayyana cewar wannan gagarumin bikin ya nuna nasarar da makarantar ke samu wajen gina ƙwararrun ma’aikatan lafiya masu kishin aiki da al'umma.

Mun jajirce wajen bai wa ɗalibai horo na zamani da ya haɗa da aikace-aikacen lissafi, kimiyya, da kuma ladabtarwa domin su fuskanci ƙalubalen aikin kiwon lafiya a Najeriya da ma kasashen waje,” in ji shugaban makarantar.

Wata daga cikin daliban da aka yaye, Fatima Mohammed, ta bayyana farin cikinta tare da godiya ga malamai bisa gudunmawar da s**a bayar wajen ganin sun kammala lafiya. Ta ce: Muna fatan mu wakilci makarantar mu da kyau a ko'ina muka samu aiki.

Bikin ya kuma haɗa da nuna bajintar dalibai ta fannonin kiwon lafiya, rera waƙoƙi da kuma gabatar da kyaututtuka ga daliban da s**a fi kowa fice a karatu da ɗabi’a.

Barumde School of Health Technology tana daga cikin makarantu masu tasowa a fannin horar da ma’aikatan lafiya a arewacin Najeriya, tana kuma samun karɓuwa daga matasa da ke sha’awar aikin jinya da lafiya.

Gidauniyar ABBA PANTAMI DATA FOUNDATION ta ziyarci gidan marayu na Al-Guh Foundation da ke cikin kwaryar jihar Gombe, in...
24/03/2025

Gidauniyar ABBA PANTAMI DATA FOUNDATION ta ziyarci gidan marayu na Al-Guh Foundation da ke cikin kwaryar jihar Gombe, inda ta taimakawa marayu da kayan abinci duba da halin maraicin da suke ciki na rashin iyaye.

Address

Kumo

Telephone

+2347037301727

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when KUMO TV posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Business

Send a message to KUMO TV:

Share