13/05/2023
SHIRYE-SHIRYEN KARBAR MULKI: Shugaba Buhari Da Iyalansa Sun Bar Fadar Shugaban Kasa
Daga Sani Twoeffect Yawuri
Shugaba Muhammadu Buhari da mai dakin sa sun bar fadar gidan shugaban kasa ta Villa zuwa wani ɓangaren gidan da ake kira Glass House.
A al'ada duk sanda za a mika mulki ga wata sabuwar gwamnati, shugaba mai barin gado zai bar Villa zuwa wannan bangaren na Glass House yayin da mika mulkin ya zo daf.
Za a gudanar da bikin miƙa mukin ne dai ga sabuwar gwamnati a ranar 29/5/2023.