23/02/2023
ZASU YAUDAREMU DA ADDINI
Daga Datti Assalafiy
Tinubu Shekarunsa 53 yana tare da Matarsa ta Aure amma bai iya Musuluntar da ita ba.
'Ya'yan Tinubu bakwai (7) banda wadanda ya haifa a waje, amma babu Musulmi ko guda daya a cikinsu.
A cikin gidan Tinubu babu Masallaci, amma akwai dakin bautar wanin Allah wanda fadin wajen ya kai kusan taku dari biyu (200).
Mutumin da idan zayyi rawa a tsaye yakeyi amma mafi yawanci a zaune kan kujera yake gudanar da Sallah cikin Masallaci, sannan bai iya karatun Fatiha ba.
Tayaya za'a yaudareka da sunan Addini ka zabi wanda babu addini a gidansa (Matarsa da 'Ya'Yansa) ballantana dabi'unsa?
Sannan idan kana maganar wai yana da kishin Arewa to ya akayi ya bada goyon baya wajen kæshe 'Yan Arewa a lokacin yana Gwamnan Lagos?
A wancan lokacin da ya k@she 'yan Arewa, Shugaban Kasar yanzu Muhammadu Buhari, ya je Lagos, ya bukaci ya gana dashi a Ofishinsa domin a kawo karshen ta'add@ncin da ake yiwa 'yan Arewa, sai Tinubu yace bai da bukatar ganin Buhari a Ofishinsa.
Ya kai dan Arewa mai hankali da tunani shin ka san da wannan abinda Tinubu yayi?
Ya kai dan Arewa wani irin Kwakwalwa kake da ita a yanzu da kake cewa zaka zabi Tinubu Shugaban Kasa saboda wai addini?
Bayan k@she rayukan 'yan Arewa Musulmi da Tinubu yayi lokacin yana Gwamna ta ina ya zama masoyin Arewa a yanzu? Ya kashe banzaye kenan ko?
Ga inda hanyar Masallaci yake, wasu azzalumai maciya amana sun karbi kudi gurin dan ta'adda suna nuna muku hanyar zuwa halaka.
'Yan Arewa masu tallen Tinubu saboda kudi, da wadanda aka yaudaresu su zabi Tinubu to ku sani har yanzu muna kaunar ku, muna fatan Allah Ya fahimtar daku hatsarin wannan mutumi ku gujeshi.