27/03/2025
Gwamna Fintiri Ya Buƙaci A Samar Da Makarantar Horar Da Ƴansanda A Jihar Adamawa
Gwamna Ahmadu Umaru Fintiri na Jihar Adamawa ya buƙaci shugaban ƴansanda na ƙasa, Kayode Egbetokun da ya samar da makarantar horar da ƴansanda a Jihar Adamawa kamar yadda ake da ita a kowace Jiha da ke shiyar Arewa maso Gabas.
Gwamna Fintiri ya yi wannan kira ne a yayin da ya karɓi baƙuncin shugaban rundunar ƴansandan wanda ya ziyarce shi a fadar gwamnatin Jihar da ke birnin Yola, kamar yadda Jaridar Mikiya ta ruwaito a wannan rana.
Gwamna Fintiri ya kuma ƙara da buƙatar neman kafa rundunar ƴansanda ta sunturi a yankin ƙaramar hukumar Madagali domin ƙarfafa yaƙi da ƴan ta’adda na Boko Haram.
Gwamnan ya kuma gode wa shugaban ƴansandan bisa wannan ziyara da ya kai masa karo na biyu tare da ba shi tabbacin ci gaba da aiki tare a tsakanin ɓangarorin biyu. Kana kuma, ya jaddada aniyar gwamnatinsa na ci gaba da tallafa wa ƴansanda da ba su duk wani haɗin-kai da goyon baya da suke buƙata wajen tafikar da aikinsu.
Tun da farko a nasa jawabin, shugaban ƴansandan, Kayode Egbetokun, ya bayyana yi wa gwamna da al’ummar Jihar Adamawa godiya a matsayin maƙasudin ziyarar tasu dangane da haɗin-kan da suke ba wa ƴansanda har ma ya bayyana Jihar Adamawa a matsayin Jihar ƴansanda inda s**a samu nasarar cimma nasarori da dama tare da taimakon jami’an tsaro na soji.