15/04/2025
Malam, da gaske ne ana cewa Salātul Fātiḥ ta fi Al-Qur’āni? Na ji wasu daga cikin Wahhābiyya na faɗa hakan, ko da yake ban taɓa jin wani Malamin Ɗarika ya ce haka ba.
Amsa:
Wallāhi wannan ƙarya ce! An juya ma’anar maganganun Malamai ne kawai don cin mutunci da ƙazafi. Ba gaskiya ba ne, kuma kuskure ne mai girma a fagen ilimi da addini.
Ga yadda Shehu Tijānī ya fayyace lamarin cikin "Jawāhirul Ma‘ānī":
Shehu ya raba masu karatun Al-Qur’āni kashi huɗu (4):
1. Qirā’atul-Kāssī (قراءة القاصي):
Wannan shi ne wanda karatun Al-Qur’āni yake gyara imaninsa, kuma hakan yana jawo shi zuwa ga Allah. Shehu ya ce wannan karatu yana da lada.
2. Qirā’atul-Kāssil-Kāssī (قراءة القاصي القاصي):
Shi ne wanda karatun Qur’āni yake jansa da zuciyarsa gaba ɗaya zuwa ga Allah. Shehu ya kawo hujja da fassarar wannan aya:
> "إِنَّمَا الْمُؤْمِنُونَ الَّذِينَ إِذَا ذُكِرَ اللَّهُ وَجِلَتْ قُلُوبُهُمْ، وَإِذَا تُلِيَتْ عَلَيْهِمْ آيَاتُهُ زَادَتْهُمْ إِيمَانًا، وَعَلَىٰ رَبِّهِمْ يَتَوَكَّلُونَ"
(Surat al-Anfāl: 2)
Haka nan kuma ya ambaci:
> "قُلْ لَئِنِ اجْتَمَعَتِ الْإِنسُ وَالْجِنُّ عَلَىٰ أَن يَأْتُوا۟ بِمِثْلِ هَـٰذَا ٱلْقُرْءَانِ لَا يَأْتُونَ بِمِثْلِهِۦ وَلَوْ كَانَ بَعْضُهُمْ لِبَعْضٍ ظَهِيرًا"
(Surat al-Isrā’: 88)
Shehu ya ce: Wallāhi babu wani abu da za ka karanta da ya kai Al-Qur’āni ko da kalma guda, duk duniya da Aljanu sun haɗu.
3. Qirā’atul-‘Āmmī (قراءة العامي):
4. Qirā’atul-‘Ammil-‘Āmmī (قراءة العامي العامي):
Wannan shi ne wanda yake karanta Qur’āni amma yana aikata sabanin abin da Qur’āni ya umarta. Shehu ya ce irin wannan karatun yana kore shi daga Allah. A nan ya ce karanta Salātin Annabi sau ɗaya ya fi irin wancabjn karatun Qur’āni sau dubu shida (6000).
Shehu ya kawo hadisin Manzon Allah (SAW):
> "رُبَّ قَارِئٍ لِلْقُرْآنِ وَالْقُرْآنُ يَلْعَنُهُ"
Ma'ana: Wataƙila akwai mai karatun Qur’āni amma Qur’ānin na la’anarsa.
To don Allah, anan Shehu ya fitar da kansa daga falalar Qur’āni ne?
Idan kana karanta abu da Qur’āni ke la’anarka, ba za ka fi wanda ke karanta Salātul-Fātiḥ ba.
Wallāhi sun karanta maganganun Shehu daga litattafansa, sai dai kawai suna ɓoyewa don a cin mutuncinmu.
Kuma idan za ka bi irin karatun da wasu ke yi, Wallāhi har Annabi (SAW) sai ka ce ya yi kuskure, alhali Manzon Allah (SAW) ya ce:
> "ركعتا الفجر خير من الدنيا وما فيها"
Ma’ana: Raka'a biyu na sallar Asubah sun fi duniya da abin da ke cikinta.
Tambaya ita ce: Shin wannan hadisin na nufin raka'o'in Asubah sun fi Annabi (SAW), Ka'aba, Al-Qur’āni, ko Sallar Farilla?
A'a! A karatun da ba da fahimta ba ne wannan.
Komai da muhallinsa. Ba a wa ilimi irin haka.
Kuma fa wasu daga cikinsu sun ce: Siyāsa ta fi Sallah!
Kuma sun yadda da hakan saboda ƙarancin ilimi da jahilci.