01/01/2023
DAGA MASARAUTAN ZAZZAU:-
Da safiyan yau Mai Martaba Sarkin Zazzau Malam Ahmed Nuhu Bamalli, CFR a Fadansa ya karbi bakuncin Hajj Zulkifili Bn Bahrum da Dokta Hajj. Shu'aib Bn Saidin daga Gidauniyar Amal na Kasar Malaysia (Gidauniyar Da take gabatar da Ayyukan Jin Kai Da Taimakon Al'umma).
Dokta Yusuf Mu'azu Shugaban Gidauniyar Abuwabul-Khair gami da sauran masu hulda da Gidauniyar Amal s**a rako bakin a lokacin gabatar da wannan ziyara.
Dokta Yusuf Mu'az da Hajj. Zulkifil Bn Bahrum sun gabatar da bayanan irin ayyukan da Gidauniyar Amal take gudanarwa a nan Nijeriya da wasu kasashe ga Mai Martaba Sarkin Zazzau a lokacin wannan ziyara.
** A yau Mai Martaba Sarkin Zazzau, Malam Ahmed Nuhu Bamalli, CFR ya Aurar da Uku daga cikin 'ya'yansa wadanda s**a fito daga gidajen Darda'u Dan Malam Musa da Banagan Zazzau da Wazirin Madauci bisa bayani Kaman haka;
I. Amarya Ummul Kulsum an daura mata aure da Angonta Malam Saifullahi wanda ya biya Naira Dubu Dari Da Hamsin ( #150,000) a matsayin Sadakinta. Sai,
II. Amarya Rabi'atu wanda aka daura Aurenta da Malam Suleiman wanda shima ya biya Naira Dubu Dari Da Hamsin ( #150,000) a matsayin Sadakinta. Sai kuma
III. Amarya Zainab wanda aka daura aurenta da Angonta Malam Abdulkadir wanda shi kuma ya biya Naira Dubu Dari Daya ( #100,000) a matsayin Sadakinta.
Malam Umar daga Anguwan Kwarbai ne ya daura dukkanin aurarrakin na yau.
*** Jami'an Kungiyan Dalibai Na Kasa 'Yan Asalin Zazzau (NAZAS), reshen Zariya da ranan yau sun gabatar ma Mai Martaba Sarkin Zazzau, Malam Ahmed Nuhu Bamalli, CFR Cekin Kudi na Naira Miliyan Daya Da Rabi ( #1,500,000) wanda Alhaji Isma'ila Yusuf Sardaunan Ikulu ya bayar a matsayinTallafi ga Dalibi Dan Asalin Zariya, Malam Ibrahim Shehu Sambo wanda ke shekaransa na karshe a Kasan Sudan domin samun daman karasa karatun aikin Likitanci da yake yi.
Mai Martaba Sarkin Zazzau dai ya mika wannan Ceki ga iyaye da Dalibin.