GARU

GARU Contact information, map and directions, contact form, opening hours, services, ratings, photos, videos and announcements from GARU, Business service, Behind korama table water potiskum, Potiskum.

25/04/2026
25/04/2026

MAKO NA BIYU {2}

NASIHA AKAN DARAJAN ILIMI

Neman ilimi hanya ce zuwa ga haske. Duk wanda ya rungumi ilimi, ya kubuta daga duhun jahilci.

Ilimi ba wai kawai yana ɗaukaka mutum a duniya ba ne, har ma yana ɗaga darajarsa a wajen Allah.

Ka sani, ilimi shi ne gado mafi daraja da mutum zai iya gada.

Dukiya na iya ƙarewa, amma ilimi yana kasancewa tare da kai har ƙarshen rayuwarka, kuma yana amfani ga al’umma bayan ka tafi.

Saboda haka, kada ka gajiya da neman ilimi ko da kuwa yana da wahala.

Malamai sun fi daraja saboda ilimi, kuma dalibai suna samun daukaka saboda ƙoƙarinsu wajen Neman Ilimi.

Duk wanda ya ɗauki hanya don neman ilimi, yana kan hanya mai albarka, domin ilimi yana shiryar da zuciya, yana gyara hali, kuma yana kai mutum ga kyakkyawar makoma.

Darasi:
Ka nemi ilimi da gaskiya da haƙuri, domin ilimi haske ne
wanda ya same shi, ya samu rayuwa mai ma’ana.

✍️Dr. Abdurrahman Sani Yakubu

25/04/2026
25/04/2026

•Haƙiƙa Kanawa jiya sun sha karatu, An zazzage hikimomi a wannan wurin, bayan haka kuma akayi raha da wasanni tsakanin malamai kowa yayi nishaɗi.

•Don ka gane waye prof Mansur a nauyin ilimi bari na baka misali: Jiya prof Sani yana Kaduna, ya gabatar Muhadarori da Ziyara, Amma kafin lokacin da prof Mansur zai gabatar da lecture har prof Sani yayi sauri ya koma kano ya halarci Lecture Prof Mansur.

•Indai prof Sani zaiyi burin sauraren Lecture Prof Mansur duk da Nauyin sa a karatu, to kai ƙaramin Alhaki kaine kafi buƙatar wannan Lecture.

a nema a saurara.

Allah yasa mudace Ameen.

25/04/2026

Good morning everyone inamuku barka da safiya inaso kugayamin wani malami kukafi Jin dadin karatun sa sheikh Albania zaria sheikhjafar Mahmud Adam sheikh Idris Abdul Aziz da sheikh gero argumgum) muhadu a comment section ).( Munarokon Allah yamusu rahama Amin

Address

Behind Korama Table Water Potiskum
Potiskum

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when GARU posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Share