Y RANO

Y RANO Contact information, map and directions, contact form, opening hours, services, ratings, photos, videos and announcements from Y RANO, Business service, YANTSAGAI LAUSU RANO L G, Rano.

Tsohon Gwamnan Jihar Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya yi kira ga Majalisar ƙasa ta yi watsi da duk wani Yunkuri da ...
18/11/2024

Tsohon Gwamnan Jihar Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya yi kira ga Majalisar ƙasa ta yi watsi da duk wani Yunkuri da zai yi wa Arewa rashin adalci ta hanyar dokokin gyaran haraji da ake son samarwa.

Kwankwaso ya yi wannan magana ne ranar Lahadi a wajen bikin kammala karatu na Jami’ar Skyline da aka gudanar a Cibiyar Ammani, GRA Nasarawa, Kano.

A cikin jawabin nasa, Kwankwaso ya zargi Lagos da kokarin mallake yankin Arewa. Ya ce akwai yunkuri mai yawa daga bangaren Lagos na neman mamaye Arewa ta hanyoyi daban-daban.

Ya kuma zargi Shugaban Ƙasa, wanda ya fito daga Lagos, da yin katsalandan a batun sarautar Kano.

Kwankwaso ya yi kira ga Majalisar Ƙasa da ta kare martabar Arewa da tattalin arzikinta ta hanyar hana aiwatar da duk wani tsari da zai kawo wa yankin asara ko rashin adalci.

Ya kamata shugabanni su yi aiki don kare muradun mutanen Arewa, maimakon barin wasu daga sauran bangarorin ƙasa su yi yunkurin tauye mana ‘yanci da martaba,"** in ji shi

Jam’iyyar PDP ta sanar a Jiya Talata cewa taron Kwamitin Zartarwa na Kasa (NEC) wanda aka shirya yi a ranar Alhamis, an ...
23/10/2024

Jam’iyyar PDP ta sanar a Jiya Talata cewa taron Kwamitin Zartarwa na Kasa (NEC) wanda aka shirya yi a ranar Alhamis, an dage shi zuwa ranar 28 ga Nuwamba, 2024.

Wannan bayanin ya fito ne a wata sanarwa da aka fitar ta Forum na Gwamnonin jam’iyyar PDP, karkashin jagorancin Bala Mohammed, Gwamnan Jihar Bauchi, bayan wani taron tattaunawa da sassa daban-daban na jam’iyyar.

Sanarwar ta ce, “Bayan wani taron tattaunawa da sassa daban-daban na jam’iyyar PDP, jam’iyyar ta yanke shawarar cewa taron Kwamitin Zartarwa na Kasa da aka shirya gudanarwa a ranar 24 ga Oktoba 2024, an dage shi zuwa ranar 28 ga Nuwamba, 2024.

“Dagewar taron na da nufin tabbatar da cewa jam’iyyar za ta shiga zabukan gwamna na Ondo da za a gudanar ranar 16 ga Nuwamba, 2024 da karfi da hade kai domin kwace mulkin jihar daga hannun Gwamnatin jam’iyyar APC da ke fama da matsaloli.

“Taron ya kuma jaddada buƙatar Haɗin kai a wannan lokaci da wasu ke ƙoƙarin raba kan jam’iyyar, Kuma ya yi kira ga dukkan ‘ya’yan jam’iyyar da su guji furucin da zai iya haifar da rashin jituwa, domin a ƙara karfafa jam’iyyar tare da shiryawa Gabannin Zabukan 2027

A safiyar yau ne shugaba Bola Tinubu yayi wata Ganawa Ta musamman Da Zacch Adedeji, shugaban Hukumar tattara kudaden har...
21/10/2024

A safiyar yau ne shugaba Bola Tinubu yayi wata Ganawa Ta musamman Da Zacch Adedeji, shugaban Hukumar tattara kudaden haraji na ƙasa FI

A jihar Kogi ma, APC ta lashe dukka kujerun ciyamomi 21 da na kansiloli 239 a zaɓen da aka gudanar a jiya Asabar.
20/10/2024

A jihar Kogi ma, APC ta lashe dukka kujerun ciyamomi 21 da na kansiloli 239 a zaɓen da aka gudanar a jiya Asabar.

Tinubu ya dawo Nijeriya bayan hutun makonni biyuShugaba Bola Tinubu ya dawo gida Abuja bayan ya shafe makwanni biyu ya n...
20/10/2024

Tinubu ya dawo Nijeriya bayan hutun makonni biyu

Shugaba Bola Tinubu ya dawo gida Abuja bayan ya shafe makwanni biyu ya na hutun aiki a kasar Birtaniya.

Tinubu ya isa filin jirgin saman Nnamdi Azikiwe dake Abuja da misalin karfe 7:20 na safe a jiya Asabar, inda ya samu tarbar manyan jami’an gwamnati.

Shugaban ya samu tarbar gwamnan jihar Legas, Babajide Sanwo-Olu da shugaban ma'aikatan fadar shugaban kasa, Femi Gbajabiamila.

Sauran sun hada da, Wale Edun (Ministan Kudi), Abubakar Atiku Bagudu (Ministan Kasafi da Tsare-tsare), Nuhu Ribadu (Mai ba da shawara kan harkokin tsaro), da Abdullahi Ganduje, shugaban jam'iyyar APC na kasa.

Bankin Duniya ya gargaɗi Nijeriya kan janye sabbin manufofin tattalin arziki da gwamnatin Tinubu ta kirkiro Bankin duniy...
17/10/2024

Bankin Duniya ya gargaɗi Nijeriya kan janye sabbin manufofin tattalin arziki da gwamnatin Tinubu ta kirkiro

Bankin duniya ya bukaci gwamnatin tarayya da kada ta sauya manufofin da aka bullo da su na gyaran tattalin arziki, yana mai gargadin cewa hakan na iya haifar da mummunan tasiri ga kasar.

Kawar da tallafin man fetur da kuma soke tsarin musayar kudaden waje ne manufofin da gwamnati mai ci ne ta bullo da su a rana ta farko da hawan ta mulki.

Yayin da gwamnatin tarayya ta ke kare manufofin, da dama daga cikin ‘yan Najeriya na kokawa da irin tasirin da suke da shi ga talakawa.

Da ya ke jawabi a wajen kaddamar da rahoton ci gaban Najeriya (NDU) a Abuja a yau Alhamis, darektan bankin duniya a Najeriya, Dr. Ndiame Diop, ya ce duk da cewa sauye-sauyen na iya kawo wahalhalu, sun zama dole domin daidaito kan tattalin arziki.

Diop ya yi gargadin cewa, "Mayar da wadannan sauye-sauyen zai yi illa kuma babbar matsala ce ga Najeriya."

A nashi bangaren, Ministan Kudi kuma Ministan Tattalin Arziki, Wale Edun, ya jaddada kudirin gwamnatin tarayya na ci gaba da bijiro da manufofi da ta ke yi.

A shirye muke mu yi Maja da jam'iyyu don kawar da APC - NNPPJam'iyyar NNPP ta ce APC ce ke daukar nauyin rikicin da ke f...
17/10/2024

A shirye muke mu yi Maja da jam'iyyu don kawar da APC - NNPP

Jam'iyyar NNPP ta ce APC ce ke daukar nauyin rikicin da ke faruwa a wasu jam'iyyun adawa a kasar nan domin ta ci gaba da rike mulki bayan shekarar 2027.

Ajuji Ahmed, Shugaban jam'iyyar NNPP na kasa ne ya bayyana hakan a taron kaddamar da yakin neman zaben dan takarar gwamna na jam'iyyar a jihar Ondo, Olugbenga Edema, da aka yi a Akure, ranar Alhamis.

Ahmed ya zargi APC da katsalandan cikin harkokin cikin gida na jam'iyyun adawa ta hanyar haddasa rarrabuwar kawuna tsakanin mambobinsu don raunana tsarin jam'iyyun da kwace iko.

A cewarsa, wannan lamari da APC ke yi na zuwa ne yayin da shugabannin jam'iyyun adawa ke shirin gudanar da "tattaunawar hade kai" don kawar da jam'iyya mai mulki gabanin babban zabe.

"APC na yin duk abin da za ta iya don lashe babban zaben 2027. Tabbas, akwai shaidu a ko'ina cewa suna katsalandan cikin sauran jam'iyyun. "Amma abin ya rage ga sauran jam'iyyun siyasa su kare mutuncinsu kuma su tabbatar sun kasance guda ɗaya don kafa jam'iyyar adawa mai karfi da zata kawar da APC kafin da bayan zaben 2027," in ji shugaban NNPP.

Ya bayyana cewa jam'iyyar APC mai mulki ta shirya mika mulki bayan gwamnatin Shugaba Bola Tinubu, yana mai jaddada cewa NNPP tana tare da jam'iyyun adawa domin kafa kawance gabanin zaben 2027.

"Saboda haka, kofar mu a bude take ta yadda idan za a samu hadin gwiwa tsakanin dukkan jam'iyyun siyasa don shiga zabe, muna shirye don hakan," in ji shugaban NNPP.

“Yan Nijeriya Ba Sa Jin Dadin Gwamnatin Tinubu”, Inji Gwamna BalaGwamnan Jihar Bauchi, Bala Mohammed, ya soki manufofin ...
17/10/2024

“Yan Nijeriya Ba Sa Jin Dadin Gwamnatin Tinubu”, Inji Gwamna Bala

Gwamnan Jihar Bauchi, Bala Mohammed, ya soki manufofin tattalin arzikin Gwamnatin Tarayya karkashin shugabancin Shugaba Bola Tinubu, yana mai cewa sun janyo karin wahala a kasar.

Yayin da yake jawabi a bikin kaddamar da rahoton Sabunta Cigaban Najeriya na Bankin Duniya a Abuja, ya bayyana cewa 'yan Najeriya ba sa jin dadin wannan gwamnati a dukkan matakai—tarayya, jihohi, da kananan hukumomi.

Ya bukaci a koma kan tsare-tsaren tattalin arziki da za su rage wa talakawa wahala, yana mai cewa kudaden da ake rabawa ba su isa ba wajen magance matsalolin da jihohi ke fuskanta.

APC na haifar da rikici a jam'iyyun adawa Domin samun nasarar Tinubu A 2027 - Inji Shugaban Jam'iyyar NNPP na ƙasaShugab...
17/10/2024

APC na haifar da rikici a jam'iyyun adawa Domin samun nasarar Tinubu A 2027 - Inji Shugaban Jam'iyyar NNPP na ƙasa

Shugaban jam’iyyar New Nigeria Peoples Party, NNPP, Ajuji Ahmed, ya yi zargin cewa rigingimun da ke kunno kai a jam’iyyun adawa a Kasar, jam’iyyar All Progressives Congress (APC) ce ta shirya don lashe zaben 2027.

A cewar Shugaban jam’iyyar NNPP na kasa, jam’iyyar za ta goyi bayan kuma ta zama jam’iyyar da jam’iyyun adawa zasu kulla kawance da jam’iyya mai mulki domin korar APC da Tinubu daga mulki.

Ahmed ya bayyana haka ne a yayin kaddamar da yakin neman zaben jam’iyyar a Akure, babban birnin jihar Ondo, gabanin zaben fidda gwani na Gwamna a jihar.

Yayin da 'yan Najeriya ke cikin matsatsin rayuwa saboda sauye-sauyen da gwamnati mai ci ta kawo, fargaba na karuwa kan y...
17/10/2024

Yayin da 'yan Najeriya ke cikin matsatsin rayuwa saboda sauye-sauyen da gwamnati mai ci ta kawo, fargaba na karuwa kan yiwuwar samun tashin hankali saboda bacin rai da ake ciki.

Yaya kuke kallon kiran da majalisar wakilai ta yi a halin da ake ciki?

Address

YANTSAGAI LAUSU RANO L G
Rano

Telephone

+2349165756255

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Y RANO posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Share