KIWON KAJI A Gar-Gajiyance

KIWON KAJI A Gar-Gajiyance Contact information, map and directions, contact form, opening hours, services, ratings, photos, videos and announcements from KIWON KAJI A Gar-Gajiyance, Business service, Kaduna, Soba.

(2)Amfanin ganyen zogale amatsayin vitamin da antibiotics, musamman lokacin brooding.
07/04/2026

(2)
Amfanin ganyen zogale amatsayin vitamin da antibiotics, musamman lokacin brooding.

(1) lesson  kiwon kaji na  Glucose  yana da matukar amfani ga kaji a ranar farko da aka kawo su wato suna day-old. Ga ka...
05/04/2026

(1) lesson
kiwon kaji na

Glucose yana da matukar amfani ga kaji a ranar farko da aka kawo su wato suna day-old. Ga kadan daga ciki amfaninsa
Samar da Kuzari Kajin da aka fito da su daga kwaye sababbi ne, kuma galibi sun yi tafiya mai nisa kafin su iso hannunka. Glucose yana ba su kuzari nan take domin su fara zirga-zirga su nemi abinci da ruwa.
Rage Damuwa canjin yanayi da jigilar kaji daga waje zuwa gida yana janyo musu matsananciyar damuwa . Glucose yana taimakawa wajen kwantar musu da hankali da kuma rage hadarin mutuwa sakamakon gajiya.
Karfafa Garkuwar Jiki
A ranar farko, jikin kaza yana bukatar karfi don ya fara yaki da kwayoyin cuta. Glucose yana taimaka wa jikin kazar wajen narkar da sauran kwai da ya rage a cikinsu, wanda hakan ke basu abinci da kariya kafin ta saba da kwayoyin abinci .
Hana Shanyewar Jiki Shan ruwan glucose yana sa kajin su wartsake su kuma samu ruwa a jikinsu cikin sauri, wanda hakan yana hana su bushewa ko yin rauni atare dasu.
Kurika bawa Kajin ku ruwan glucose aranar farko domin samin kuzari mai kyau da war ware gajiya ,idan gajiya r bata sake su a ranar farko to ku kara musu a rana ta biyun, Amma kada a wuce kwana biyu Ana basu shi .

Assalamualaikum in Sha Allah zamu fara karatu daka farkon saka kaji, zuwa mu fitar da su , muka sance tare
03/04/2026

Assalamualaikum in Sha Allah zamu fara karatu daka farkon saka kaji, zuwa mu fitar da su , muka sance tare

Kudaure ku gwada kiwon kaji na organics.Kilo 5½ Alhamdulillahi sati 8 da kwana 2 ,kiwon gargajiya zallah.
19/03/2026

Kudaure ku gwada kiwon kaji na organics.
Kilo 5½ Alhamdulillahi sati 8 da kwana 2 ,kiwon gargajiya zallah.

Shi kataba haduwa irin wannan cutar na taruwar ruwa acikin kaji 🦻👇👇👇
17/03/2026

Shi kataba haduwa irin wannan cutar na taruwar ruwa acikin kaji 🦻👇👇👇

Idan kana son kajinka s**a sance cikin nutsuwa  kamar haka Kuma yayin da ake zafi to ka gwada wannan 👇👇👇
14/03/2026

Idan kana son kajinka s**a sance cikin nutsuwa kamar haka Kuma yayin da ake zafi to ka gwada wannan 👇👇👇

GA wasu shawarwarin da zaka/ki kare kanka/ki daga irin wannan mutuwar a lokacin zafi👇👇👇👇
14/03/2026

GA wasu shawarwarin da zaka/ki kare kanka/ki daga irin wannan mutuwar a lokacin zafi👇👇👇👇

Shin wani mataki kake dauka ma kajinka acikin wannan yanayin na zafi, nidai ga yadda nake yi👇👇👇
12/03/2026

Shin wani mataki kake dauka ma kajinka acikin wannan yanayin na zafi, nidai ga yadda nake yi👇👇👇

Ga wasu muhimman shawarwari da za su taimaka maka ka kare su:1. Samar da Ruwa Mai Sanyi da TsaftaRuwa akai-akai: Tabbata...
09/03/2026

Ga wasu muhimman shawarwari da za su taimaka maka ka kare su:
1. Samar da Ruwa Mai Sanyi da Tsafta
Ruwa akai-akai: Tabbatar kajin suna da ruwa mai sanyi a gabansu sa'o'i 24. A lokacin zafi, kaji suna shan ruwa kusan ninki biyu na abincin da suke ci.
Kankara: Idan zafin ya tsananta (tsakanin karfe 12 na rana zuwa 4 na yamma), za ka iya sanya kankara kadan a cikin ruwan shan su domin ya rage musu zafin ciki.
2. Canja Tsarin Ciyarwa
Lokacin Ciyarwa: Kada ka ciyar da kaji a lokacin da rana ta yi zafi sosai. Zai fi kyau ka ba su abinci da sassafe (kafin 10 na safe) da kuma yamma (bayan 5 na yamma).
Cire Abinci: Yawancin makiyaya suna janye kwanukan abinci daga karfe 11 na safe zuwa 4 na yamma don gujewa narkar da abinci (digestion) wanda ke kara wa kaji zafi a jiki.
3. Samun Iska (Ventilation)
Budadden Dakali: Tabbatar dakin kaji yana da tagogi da iska ke ratsawa sosai. Idan dakin yana da labule, ka bude su gaba daya a lokacin zafi.
Yawan Kaji: Kar ka cika kaji da yawa a daki daya. Rage yawan kajin da ke cikin kowane bangare domin kowacce ta samu sararin shakar iska.

DARASIN YAU:-MATSALAR ZAFI GA KAJIZafi na faruwa idan yanayin zafi ya yi yawa har kaji ba su iya daidaita jikinsu. Wanna...
08/03/2026

DARASIN YAU:-

MATSALAR ZAFI GA KAJI

Zafi na faruwa idan yanayin zafi ya yi yawa har kaji ba su iya daidaita jikinsu. Wannan yakan faru musamman lokacin rana mai zafi wannan na takurawa Kaji fiye da yadda muke tunani don yadda kuke Ganin Kaji na mutuwa ba tare da wani Cutaba toh Zafi na daga cikin Abunda ke kashe Kaji cikin Yan mintina, don Abunda ke faruwa shine idan Ana tsananin Rana zafin Yana narkar da kitsen jikin kajinne Wanda Kunsan Kaji Musamman Broilers da kitse toh wannnan kitsen idan ya narke sai ya malala akansu wato sai ya hau musu Kai Wanda ke sanadin mutuwansu nan take.

ALAMOMIN MATSALAR ZAFI GA KAJI

*Kaji suna bude baki suna haki

*Suna shimfiÉ—a fikafikai domin samun iska

*Rage cin abinci

*Yawan shan ruwa

*Suna zama kasa suna kasala

*A wasu lokuta mutuwa ba zato

ILLOLIN MATSALAR ZAFI

Raguwar girman broilers
Yawan Kashi Mai Ruwa zallah
Raguwar yawan kwai ga layers
Raguwar karfin garkuwar jiki
Yawan mutuwar kaji

YADDA ZA A RAGE MATSALAR ZAFI

#. Iska mai kyau (ventilation)

#. Ka tabbata gidan kaji yana samun iska sosai.

#. Ruwa mai sanyi kullum

#. Ka tabbatar kaji suna da ruwa mai yawa a koda yaushe.

#. Vitamin C a ruwa, yana taimaka musu su jure zafi.

#. Kada a cunkushe kaji, A ba su sarari a cikin gidan kaji.

#. Sanya fanka Inda hali, Domin rage zafin ciki.

#. Ciyar da su da safe ko yamma, Kada a ciyar da su lokacin rana mai tsananin zafi.

#. Shuka bishiya kusa da gidan kaji, Domin inuwa ta rage zafi.

#. Wani magani mai sauki, Vitamin C + Glucose a cikin ruwa lokacin zafi yana taimaka sosai .

copied

Address

Kaduna
Soba

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when KIWON KAJI A Gar-Gajiyance posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Share