23/01/2021
Assalamu alaikum wa rahama tullahi wabara katuhu An karɓo daga Umar (R.A) ya ce, "Yayin da muna zaune a wurin Annabi (ﷺ) wata rana, sai wani mutum ya bayyana gare mu, mai tsananin farin tufafi, mai tsananin baƙin gashi, kuma ba a ganin alamun tatiya tare da shi, kuma a cikinmu babu wanda ya san shi, har ya zauna kusa da Annabi (ﷺ) ya jingina gwiwowinsa guda biyu zuwa ga gwiwowin Annabi (ﷺ), ya ɗora tafukan hannunsa a kan cinyoyinsa, sai ya ce, "Ya Muhammad! Ba ni labari game da musulunci." Sai Annabi (ﷺ) ya ce, "Muslunci, shi ne ka shaida babu abin bautawa bisa ga cancanta, sai Allah, kuma Muhammad (ﷺ) Manzon Allah ne, ka tsayar da sallah, ka ba da zakka, ka yi azumin watan Ramadan, ka ziyarci ɗakin Allah in ka sami iko." Sai ya ce, "Ka yi gaskiya!" Sai muka yi mamakinsa, saboda yana tambayarsa, kuma yana gasgata shi. Sai ya ce, "Ba ni labarin Imani." Sai ya ce, "Ka yi imani da Allah, da Mala'ikunsa da Littattafansa, da Manzanninsa da ranar lahira, kuma ka yi imani da ƙaddara alherinta da sharrinta." Sai ya ce, "Ka yi gaskiya!" Sai ya ce, "Ba ni labarin kyautatawa." Ya ce, "Ka bauta wa Allah kamar kana ganinsa, idan ba kaganinsa, to shi yana ganinka." Ya ce, "Ba ni labarin alƙiyama." Sai ya ce, "Wanda aka tambaya, bai fi mai tambayar sani ba." Sai ya ce, "Ba ni labarin alamominta." Sai ya ce, "Baiwa ta haifi uwargidanta, kuma ka ga mutane marasa takalma, matsiraita, talakawa, masu kiwon dabbobi, suna tsawaita gine-gine." Sai (mutumin), ya tafi, muka zauna lokaci mai tsawo, sannan sai Manzon Allah (ﷺ) ya ce, "Ya Umar! Ko ka san mai tambayar nan? Sai na ce, "Allah da Manzonsa su ne s**a sani" Sai ya ce, "Haƙiƙa Jibrilu ne ya zo muku don ya koya muku addininku." Muslim ne Ya rawaito shi