Auwalu muhammad koleju

Auwalu muhammad koleju Contact information, map and directions, contact form, opening hours, services, ratings, photos, videos and announcements from Auwalu muhammad koleju, Business service, SOKOTO north Katu bakwa opposite federal house, Sokoto.

06/07/2021
14/07/2019

Macen Da Ke Da Wuyar Samu A Yau

Daga Sheikh Aminu Ibrahiim Daurawa
__________________________________

Ya kamata mu sani cewa mace daya ce a duniya take da wuyar samu, amma idan ka samu irinta, kada ka kuskura ka rabu da ita. Ya halatta ka auri mace fiye da daya, amma ka sani, mace daya ce kawai, ta ke yin tasiri a rayuwa, wacce ranka kullum zai kasance a kanta.

Babbar tambaya a nan ita ce, wacece wannan dayar? Ita ce wadda duk da namiji yake muradin samu a rayuwarsa, Ita ce wadda ke koyi da rayuwar shugabar matan duniya kuma diya ga Rasulallahi (SAW), wato Nana Fatima (Allah Ya kara mata yarda).

Haka kuma ita ce wadda kowace mace take fata ta zama.

Ga siffofinta guda goma, kamar.
haka:

1. Matar da ta yarda ita mace ce, don haka ta tanadi duk abin da ake bukata a wajan mace.
2. Mace mai hikma da azanci, wacce ta karanci mijinta da kyau, kuma take kaucewa duk abin da
zai haddasa matsala a tsakaninsu.
3. Mace mai taushin hali da nutsuwa, wacce miji yake jin nutsuwa, idan yana tare da ita.
4. Mace da kudi bai dame ta ba, ita mijinta kawai take so, ko da akwai ko babu.
5. Mace mai hakuri da juriya, babu gunaguni, babu mita, da kai kara ga iyaye ko kawaye.
6. Macen da ta dauki kanta likita, mijinta mara lafiya, domin ya sami kulawa, ta musamman da.
riritawa.
7. Mace mai saurin daukar ishara, tana gane shiru da magana, da motsi da yanayin shigowa da
fita, samu da rashi da kuma yanayin da ake ciki a duniya ko a gari.
8. Mace mai sakakkiyar zuciya, mara kulli da ramuwa.
9. Mace mai karawa miji kuzari da karfin hali, a kan kyawawan manufofinsa.
10. Mace mai rikon amanar aure, da soyayya ga mijinta kawai.

Fatanmu ubangiji yasa mudace da mata na Kwarai.

14/07/2019

Sunnah

Alwalar annabi saw
14/07/2019

Alwalar annabi saw

SIFFAR ALWALAR ANNABI (SAW)

( Ayi mana afuwa a rubutun farko akwai kuskure (typing error ciki.( Manzon Allah yakan shafi kansa da kunnuwansa sau d'aya ne..)

_________maimaici๐Ÿ‘‡

โœฟ Farko yana wanke tafukan hannunsa sau uku, tare da yin niyya.

โœฟ Sannan sai ya kuskure bakin sa ya shaka ruwa sau uku uku (da kanfata uku)

โœฟ Sai kuma ya wanke fuskar sa sau uku

โœฟ Sannan ya wanke hannayensa zuwa gwiwar hannu sau uku, yana farawa da hannun dama

โœฟ Sai kuma ya shafi kansa da kunnuwansa sau daya

โœฟ Sannan sai ya wanke kafafuwan sa sau uku, yana farawa da kafan dama.

Yana karanta wannan Addu'ar bayan ya gama alwalla;

ุฃุดู‡ุฏ ุฃู† ู„ุงุฅู„ู‡ ุฅู„ุง ุงู„ู„ู‡ ูˆุญุฏู‡ ู„ุงุดุฑูŠูƒ ู„ู‡ุŒ ูˆุฃุดู‡ุฏ ุงู† ู…ุญู…ุฏุง ุนุจุฏู‡ ูˆุฑุณูˆู„ู‡ุŒ ุงู„ู„ู‡ู… ุงุฌุนู„ู†ูŠ ู…ู† ุงู„ุชูˆุงุจูŠู† ูˆุงุฌุนู„ู†ูŠ ู…ู† ุงู„ู…ุชุทู‡ุฑูŠู†"

Ash_hadu an-la'ila ha illallahu wahdahu laa sharika lahu, wa ash_anna Muhammadan 'abduhu warasuluhu, Allahumma j alniy minat_tawwabina waj_alni minal mutatahhirina"

Fassara: Ina shaidawa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, shi kad'ai, babu abokin tarayya a gare shi: kuma ina shaidawa cewa Muhammadu bawansa ne kuma manzonsa ne.Ya Allah ka sanya ni a cikin masu yawan tuba, kuma ka sanya ni a cikin masu tsarkaka.

NB: Ana so duk sanda mutum ya yi alwallah, ya yi sallah raka'a biyu (Ana kiranta NAFILAR ALWALLA).

Tsokaci:
Ku Sani ya jama'a, ita alwala wata hanya ce ta kankarar zunubai. Amma se ana yinta irin alwallar Annabi (SAW).

Allah Ta'ala yasa mu dace.

Telegram: https://t.me/Fisabilillaaah

9/7/2019

_____________________

Allah kanunama Ranar Gaisawa Tsakanin Manumi๐Ÿ๐Ÿ‰๐Ÿ†๐Ÿ‡๐Ÿ“๐Ÿ’๐ŸŒด๐ŸŒท da makiyayi๐Ÿ‚๐Ÿƒ๐Ÿƒ๐Ÿ‚ Acikin farin ciki๐Ÿ˜๐Ÿ˜€๐Ÿ˜๐Ÿ˜€
23/09/2018

Allah kanunama Ranar Gaisawa Tsakanin Manumi๐Ÿ๐Ÿ‰๐Ÿ†๐Ÿ‡๐Ÿ“๐Ÿ’๐ŸŒด๐ŸŒท da makiyayi๐Ÿ‚๐Ÿƒ๐Ÿƒ๐Ÿ‚ Acikin farin ciki๐Ÿ˜๐Ÿ˜€๐Ÿ˜๐Ÿ˜€

23/09/2018
Allah kaji tausayinmu
23/09/2018

Allah kaji tausayinmu

Allah kayi mana Mafita a kasarmu Nigeria kasarmu tana cikin cakwakiya
09/07/2018

Allah kayi mana Mafita a kasarmu Nigeria kasarmu tana cikin cakwakiya

Address

SOKOTO North Katu Bakwa Opposite Federal House
Sokoto

Telephone

+2349033334757

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Auwalu muhammad koleju posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Share