28/08/2015
ME ZA'AYI YAU MAI GIDA? ''YACE KUNU''
Wani saurayi ne yayi aure sai ya gayyato
abokanshi dan su zo gidanshi agaisa da amarya,
a kuma ci abinci asha ruwa. Ango kam ya gama
hada kan abokanai, harma gori yake, yana gadara
akan kowa yazo fa. Ita amarya batasan komai ba, sai ga ango da abokanai sunzo, s**a zauna a
Falo. Ya akayi, ango ya shiga ciki ya samu
matarshi yace gamu mun iso fa, angama hada
abincin?
Daga buda bakin amarya tace ''mtsew!! nifa ba
abinda na dafa a cikin gidan nan yau, kawai na dama KUNU ne dan shi nake sha'awan nasha'',
ango ya rasa me zaice mata, yace shikenan.
Ango ya fito, ya sami abokanai, yace kutashi
muje, s**ace ina zamu? yace kuzo mu tafidai,
s**a tashi, da akaje waje ya musu bayani dalla-
dalla, ya basu hakuri akan abunda ya faru. A'ah!!!Ango fa abun ya dameshi, washe gari zai
fita, amarya tace ''maigida kudin cefene fa'' yace
ayi KUNU, gari ya sake wayewa, zai fita, tace mai
gida me za'ayi yau, yace KUNU. Akayita jera
kuna, shi kuma ba sha yake ba, zuwa waje yake
ya ci abincinai. Amarya tace gida yafi nan, ba sai ta tafi ba. Ta
isa gida Babanta ya ganta, sai yayi zaton wuni
tazo, "ya akayi bata tafi ba hardare ya fara yi",
sai ya kira mijin yace meke faruwa? Mijin ya
bashi labarin abunda ya faru. Sai uban yace kada
yazo, Kuma kada ya nemeta a waya. Gari ya waye, baba zai fita, sai matarshi tace mai gida
me za'ayi yau a gidan, yace ''KUNU'', washe gari
haka, akayi ta jera kunu.
Amarya tagafa abunfa yayi yawa wai shege da
hauka, sai ta sami baba ta gaishe shi.
Tace zata koma gidan mijn ta, yace shike nan, Allah kiyaye. Tana isa mijin bai dawo ba sai dare,
da ya dawo ya sameta, yace kin dawone? tace
eh, yace yayi kyeu, washe gari zai fita, tace mai
gida baka bada kudin cefene ba, sai yace KUNU
za'ayi.
Kawai sai ta fashe da kuka, tayita bashi hakuri cewa tayi kuskure kuma bazata karaba.hahahhah
a kaima in kayi dariya KUNU zaka tarar a gida