21/02/2024
Wasu abokai guda biyu sun yi tafiya, sai s**a sauka a wani Hotel..
Bayan sun tashi da safe, sai ɗaya ya rasa dirhami 100 ɗin shi da ya zuba a aljihun shi..
Sai ya tambayi ɗayan abokin shi" Shin ka ga kuɗi na dana saka a aljihu.?.
Abokin nasa ya ce nine na ɗauka" Na tashi cikin dare, na fita na yi siyayya da su, zan baka idan mun fita..
Sun zo daf da ƙofar fita daga Hotel ɗin, sai mai aikin shara ya ce da su" Na tsinci dirhami 100 a ƙofar ɗakin ku jiya..
Mai wannan kuɗi ya kalli abokin shi ya ce da shi " Ka ce kai ka ɗauka.?.
Abokin ya ce " Mu biyu ne a ɗakin, da na ce ban gansu ba, da sheɗan ya samu damar shiga tsakanin mu..
Shi yasa na gwammace na ce ara na yi, don kada mu rasa abotar mu ta dalilin yan wasu kudaɗe..
ALLAH ka bamu abokai na gari.🙏👏🙏
✍️ عباد الرحمن