Sani salisu Darma

Sani salisu Darma Domin tattaunawa akan Al'amuran yau da kullum musanman bagaren siyasa da kasuwancin da Addini muhawara ,labarai , fadakarwa da nishadan tarwa

22/08/2026

Wani sabon bayani da Maikano Sorondinki ya wallafa ya jawo hankali kan makomar Durbar Mauludi da rikicin masarautar Kano.

A wani rubutu da ya wallafa a shafinsa na Facebook, Mai Kano Sorondinki ya bayyana cewa akwai bayanan da ke nuna cewa Mai Martaba Sanusi Lamido Sanusi na shirin gudanar da jerin gwanon Durbar Mauludi a Kano a ranakun Litinin 24 da Talata 25 ga Agusta 2026.

A cewarsa, wannan shiri ya biyo bayan wasu shirye-shirye da ake zargin Mai martaba sarkin Aminu Ado Bayero ya yi na gudanar da Durbar a ranakun.

Mai Kano Sorondinki ya kuma yi ikirarin cewa Sanusi Lamido Sanusi ya tattauna da Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, inda aka ba shi damar gudanar da wannan shiri.

Bugu da ƙari, rubutun ya yi zargin cewa ɓangaren Kofar Kudu na shirin tattaro magoya baya daga ƙananan hukumomi 44 na jihar domin gudanar da zanga-zanga kan Matsayin Mai Bai wa Shugaban Ƙasa Shawara kan Harkokin Tsaro (NSA), bisa zargin goyon bayan Aminu Ado Bayero da samar masa da tsaro.

Sai dai, Gambiza Tv ta jaddada cewa waɗannan bayanai zarge-zarge ne da ke cikin rubutun Mai Kano Sorondinki, kuma ya kamata a jira tabbacin hukumomin da abin ya shafa kafin ɗaukar su a matsayin tabbataccen lamari.

Mai Kano Sorondinki ya kuma yi kira ga magoya bayan Sarkin kano Alh Aminu Ado Bayero da su kasance cikin taka-tsantsan, tare da guje wa duk wani mataki da zai iya haifar da rikici ko tashin hankali.

A ra'ayinku, ya kamata hukumomin tsaro su ɗauki waɗanne matakai domin hana rikici tsakanin magoya bayan ɓangarorin masarautar Kano?

Domin samun ƙarin labaran Kano, siyasa da sauran muhimman abubuwan da ke faruwa a Najeriya, ku ci gaba da bibiyar Gambiza TV.

21/08/2026
14/08/2026

Ƴar gwagwarmayar siyasa, Teemah Cool, ta yi wani zazzafan bayani kan yadda alaƙarta da Rabi’u Musa kwankwaso ta shafi salon siyasarsu.

A cewar Teemah Cool, Rabi’u kwankwaso abokin sana’arsu ne ta siyasa, kuma ya sha zaunar da su yana koya musu cewa duk wanda ya taɓa “maigidan” su a siyasa, su rama.

Ta ce bayan komawarsu APC, lokacin da wasu s**a fara s**ar gwamnan da suke goyon baya, sai s**a mayar da martani da waƙar “Ɗan Kamfan Tsula.”

Maganar ta haifar da ce-ce-ku-ce a tsakanin masu bibiyar harkokin siyasa. Shin wannan dabarar siyasa ce ko kuma siyasar ramuwar gayya?

Ku fa, me za ku ce?

📺 Gambiza Tv — Muryar Labaran Arewa.
Ku biyo Gambiza TV domin samun labarai, siyasa da abubuwan da s**a shafi al’umma cikin Hausa.

13/08/2026

Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, ya koma jam’iyyar APC ne daga NNPP, inda ya tarar da ’yan jam’iyyar APC da s**a yi fafatawa da shi a zaɓen 2023.

Bayan komawarsa APC, a watan Janairu an raba babura 600 ga masu tasiri a kafafen sada zumunta da masu ƙirƙirar abubuwan digital.

Yanzu kuma gwamnatin ta sake yin rabon filaye ga yan Yan social media, ciki har da masu aiki a kafafen sada zumunta da wasu da ke taimaka wa gwamnatin wajen yaɗa ayyukanta.

Rahotanni sun ce an raba sama da filaye 2,000 cikin kwanaki biyu, yayin da wani ɓangare ya shafi masu taimaka wa gwamnati da ’yan social media.

Amma tambayar da Gambiza TV ke jefa wa jama’a ita ce:

Tun da Gwamna Abba ya shigo APC, shin tsoffin ’yan APC da s**a yi wa jam’iyyar aiki kuma s**a fafata da shi a 2023 suna samun irin wannan kulawar?

Ko kuwa wadanda s**a biyo Gwamna Abba daga NNPP zuwa APC ne s**a fi samun rabon moriya?

Mu bar wannan tambayar a hannun ’yan Kano.

Ku ne za ku ba mu amsar: Tsoffin APC sun samu, ko sabbin APC ne s**a fi samun kulawa?

Gambiza Tv — Muryar Jama’a, Labarin Gaskiya.

04/08/2026
31/07/2026

A wani rubutu da ya wallafa a shafinsa na Facebook, Farouk Abba Labaran ya ce, a ra'ayinsa, Pantami ma ya taɓa yin kalamai masu zafi kan waɗanda ba sa cikin jam'iyya ɗaya da shi, don haka bai ga abin mamaki ba idan yanzu wasu s**a mayar masa da martani.

Sai dai wannan ra'ayi na Farouk Abba Labaran ne, kuma ba lallai ya wakilci ra'ayin kowa ba.

A gefe guda, Pantami ya taɓa jaddada cewa yana mutunta ra'ayin kowa tare da nesanta kansa daga wasu kalamai masu zafi da aka taɓa wallafawa a shafinsa na Facebook, yana mai cewa ba su samu amincewarsa ba.

Majiyar labari: Rubutun Farouk Abba Labaran da ya wallafa a shafinsa na Facebook.

Ku ci gaba da bibiyar Gambiza Tv domin samun sahihan labarai, rahotanni da sharhi cikin harshen Hausa. Kada ku manta ku yi follow, ku yi sharing domin labarai su isa ga sauran al'umma.

Me kuke tunani?

Shin ya dace a mayar da martani da zagi a siyasa, ko kuwa ya kamata a riƙa mayar da martani cikin hujja da mutunta juna?

Address

Woji Street
Woji

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Sani salisu Darma posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Business

Send a message to Sani salisu Darma:

Shortcuts

Share