Abba ali Commander - SAC

Abba ali Commander - SAC Contact information, map and directions, contact form, opening hours, services, ratings, photos, videos and announcements from Abba ali Commander - SAC, Aerospace Company, Yakasai.

01/12/2023

May the exceptional favour and unending grace and mercy of Allah (SWT) be with you today and forever. May the power of Almighty Allah continue to lift us and our loved ones above all the challenges of life. May Allah SWT give us wisdom, courage, determination, prosperity, good health, long life and protect us and our families from all calamities and misfortune... .....Ameen Ya Rabbil Alameem.........Jumaat Mubarak 🕌🕌🕌🕋🕋🕋📿📿📿

Idan mai karatu bai mantaba a darasinmu na baya wato darasi na Hudu (4) mun tsaya akan yanda zakuyi backup na stock cust...
13/07/2018

Idan mai karatu bai mantaba a darasinmu na baya wato darasi na Hudu (4) mun tsaya akan yanda zakuyi backup na stock custome Rom din wayarku to yau insha Allah zamu dora darasi na biyar(5) kuma shine darasi na karshe, wato wannnan darashin shine na yanda zaka dora kowane irin file/verion akan wayar taka ta android, tunda abaya munyi bayanin yanda zaku ajiye ainihin file/rom din wayar taku akan memory da kuma yanda zaku dawo dashi ainihin kan wayar
Yauwa k**ar de yanda abaya nayi bayanin yanda zaku sanya Recovery img da kuma yanda ake shiga Recovery akowace irin waya, sannan nayi bayanin yanda zaku ajiye Rom/file dinku akan memory da kuma yanda zaku dawo dashi, idan baku mantaba duk wannan abubuwan daya zayyano nace anayinsune ta hanyar shiga Recovery ina fatan mai karatu yana biye damu,
Yauwa to yanzu abun da zakuyi shine, kuje google kuyi download na Rom din da kukeso ku dora a wayar taku misali kuna da android version 4.4 kitkat, k**ar su Y2 Y3 da sauransu to kukuma kunaso ku mayar da ita version 5.0 lollipop k**ar su gionee p5 ko tecno c8, to idan zakuyi download na Rom din saiku Rubuta a google k**ar haka,
Misali kana da waya Tecno Y2 kanaso ka mayar da ita version 6 marshmallow, to saika Rubuta k**ar haka Download tecno y2 6.0 custom rom, duk rom din wayar da zaka dauko haka zakayi da zarar kayi haka insha Allah zasu baka shi, sai kayi download dinsa ammafa, suna da nawi dan haka saika dan nemi Data/mb mai dan yawa,
Bayan kunyi download dinsa saiku ajiyeshi akan memory dinku, akan memory fa kada ku dorashi akowane folder kawai akan memory, da zarar kun gama dorashi akan memory, shikkenan yanzu saiku sanya wayar taku a Recovery domin sanya wayar saiku saika kashe wayar taka. Sannan yanzu saika kunna idan ka tashi kunna wayar saika danne Madannin kunna wayar tare
da wajen Kara Volume na wayar duk ka dannesu a lokaci daya, wato wajen kunna waya da wajen kara volume su zaka danne. Da zarar ka danne bayan wadansu seconds zata kawo sannan zata kawoka cikin Recovery dinnan daka dora to karka damu yayin data kawo zakaga ta nuno Rubutu k**ar haka:
--reboot system now
--Install Zip From SDcard
--Wipe data/factory Reset
--Wipe cache Partition
--backup and restore
--Mounts & Storage
--Advance
Wannan Rubutun da ta jero sune Recovery din daka dora to yanzu abin da zakayi saika shiga Inda aka Rubuta: Install Zip From SDcard idan ya bude saika Shiga inda aka Rubuta
Choose zip From Sdcard da zarar ya bude zakaga ta jeroma foldodi na Memory dinka, to karka damu ka duba Zakaga wannan Rom din da kayi download wanda nace ka ajiyeshi akan memory, to da zarar ka ganshi sai kaje kansa ta hanyar danna madannin Rage volume, da zarar kahau kansa, saika danna wajen kunna wayar da zarar ka danna nan Ta ke zakaga ta fara dora maka wannan Rom din, to saika jira har saita gama, amma tana dan daukan Lokaci dan haka karka damu, kawai ka jira ta gama, idan ta gama zata nunama Install Complate shikkenan file ya doro, yanzu saika duba inda aka Rubuta reboot system now saika Shiga daka shiga zakaga wayar ta kunnu, shikkenan tana kunnuwa zakaga sauyi, domin kuwa nan take zakaga komi na wayar ya chanja, tun daga kan Boot animation har boot sound, duk tsarin wayar taka zai koma na sabon Rom din daka, dora misali idan wayar taka Version 4 ce kitkat, to da zarar ka gama install na rom dinnan nan take, zakaga ta koma rom din daka dora idan rom din marshmallow ka dora to zakaga wayar ta juya zuwa mashwollow, kuma kaima daga yanzu insha Allah duk abin da mai version 6 zaiyi kaima zakayi.
Ina fatan kun gane wannan darasin
Yanzu ga yanda zaku dawo da ainihin rom dinku, wato yanda zaku dawo da wayarku zuwa ainihinta misali wayarku version 4 ce sai kuka mayar da ita version 5 ko 6, kuma sai kuka gaji da version din kode wani abun dabam to ga yanda zaku dawo da Rom din, naku.
Idan baku mantaba a darasinmu na baya, wato darasi na 4 munyi bayanin yanda zakuyi Backup na
stock/custome Rom na wayarku ta android wato yanda zaku ajeye ainishin rom din wayar taku,
To wannan Rom din da mukayi bayin yanda ake ajiyeshi to shine ainihin wayar taku yayin da kuka chanja wani rom din kuma daga baya kukeso ku dawo da ainihin naku, to shide wanda mukayi bayanin abaya to shine wanda zaku dawo din dashi dan haka ga yanda zakuyi ku dawo dashi
Da farko ku sanya wayar taku a Recovry mun riga mun fadi yanda ake sanya waya a recovery wato akashe waya idan an tashi kunnawa sai a danne madannin kara volume da kuma wajen kunna wayar duk a lokaci daya da zarar an danne zata kawoku nan wato zata jero irin wannan rubutun na kasa to saiku shiga
--reboot system now
--Install Zip From SDcard
--Wipe data/factory Reset
--Wipe cache Partition
--backup and restore
--Mounts & Storage
--Advance
Saiku shiga --backup and restore da zarar kun shiga zakuga inda aka
Rubuta ==> Restore

17/04/2018

YADDA ZAKU KARE LAFIYAR IDANUN KU DAGA CUTAR DAKE FITOWA A [ SCREEN LIGHT} DIN WAYAR KU
Idan har kana amfani Da waya karkai wasa Da wannan post din
Zai maka amfani
Jama,a barkan mu da wannan lokaci
barkan ku da sake kasance wa tare dani a daidai
wannan lokaci
darasin da zan gabatar muku yau yana da matuqar amfani musan man
A wajen masu yawan amfani da waya
shin ko kunsan akwai wasu cututtuka masu mugun hadari ga lafiyar idanu masu fitowa daga
Light Screen na wayar ku
akwai wani haske wanda ake kiransa da Blue Light Color
wanda wannan haske yana da hadari ga idanuwan mu,
na musan man masu ilimin kimiyya da s**ai bincike tare da kawo wasu
manhaja wato applications] wanda xasu da katar da wannan fitowar hasken mai suna Blue Light color mai dauke da kwayoyin cuta wanda idanu basu iya ganin su
wannan post dinfah yana da amfani domin a shawarce ka dauke ka gwada amfani da wannan
hanyar dana bayar
Da farko ka shiga {Play Store}
na wayar kai seach
EYES PROTECTOR
Ko ka shiga nan
http://apk.apkmonk.com/apks-12/com.kapron.ap.eyecare_2018-01-12.apk?X-Amz-Algorithm=AWS4-HMAC-SHA256&X-Amz-Credential=IFVYHACUO60QSGWW9L9Z%2F20180416%2Fus-east-1%2Fs3%2Faws4_request&X-Amz-Date=20180416T195009Z&X-Amz-Expires=2400&X-Amz-SignedHeaders=host&X-Amz-Signature=cdaf3496fb4aa7324ca4d191ced01be54a41135007a8f4fa9bb6916f0bf3a11f
bayan ka dauko ka bude sai ka kunna shi
anan take xaka ga yanayin Light Screen dinka ya sanja
wato wannan application din ya dakatar da wannan Blue light color din
ina fata kowa ya fahimta
Allah bada sa,a
Posted By = Suleiman Telecoms Zango STZ
WhatsApp Number +2348081888188

17/04/2018

[Android] TAMBAYOYI BAKWAI 7 GA MAI AMFANI DA WAYAR ANDROID YA KAMATA YASAN AMFANINSU
Android wacce ake furta ta da
Hausa anduroyid manhaja (OS) ce
da kamfanin Google Media Inc da ke kasar Amurka ya mallaki
lasisinsa wanda shi wannan
manhajar ake amfani da ita a kan
wayoyin hannu da kuma ƙananan
kwamfutocin hannu da ake kira
da Table PC. Su irin wannan wayoyi na Android ba k**ar sauran waya ba ce kasancewar ita tsarin riƙe ta da tsarin amfani da ita ba a ko’ina
ake yi ba. Shi ya sa na ga ya dace
in yi mana bayanai a kan waɗansu tambayoyi guda bakwai
da ya k**ata mai amfani da
waɗannan wayoyi ya sani kuma
ya san yadda zai amfani da ita.
(1) Dole ne sai na yi amfani da
Google Accout kafin in iya amfani da Android?
Haka yake! Dole duk wanda ya
sayi waya ko kuma tablet ya
zama yana da account tare da
kamfanin google kafin ya yi
amfani da ita. Amma wannan ba yakebance cewa akwai wani
ɓangare na google accout wanda
ya zama wajibi ne a ce shi ne
mutum zai yi amfani da shi ba.
Abin da ake so kawai ka yi rajista
da kamfanin ta wurin mallakar ɗaya daga cikin abubuwan da
suke gabatarwa na ayyukansu,
k**ar gmail da mak**antansu.
Kodayake google yana ba mutum
damar kara wani imel wanda ba
google ba, sai dai duk lokacin da mutum yake son ya shiga ya ƙara
wa wayar tashi ko tablet dinshi
kuzari ko kuma ya kara mata
wani application, to dole sai in
yana da account tare da google.
Kuma akwai waɗansu abubuwa masu matukar amfani ga mai
amfani da wayar android ko
tablet wanda idan mutum ba ya
amfani da account na google ba
ne, to ba zai same su ba.
(2) Wace hanya ce ta fi kyau wacce zan bi in kwashe duk
sunayen da suke cikin wayata?
Akwai hanyoyin da mutum zai iya
bi domin ya ga ya kwafe tsofaffin
lambobin cikin wayarsa zuwa
wayarsa ta android. Ɗaya daga cikin hanyar shi ne mutum zai iya
buɗe google sai ya shiga dakin
aikawa da sakon imel wanda ake
kira da gmail, to sai ya rubuce
dukkanin sunayen da ke wayarsa
daga nan lambobin da kansu za su dawo cikin wayarsa ko kuma
tablet pc ɗin shi. Ko kuma ka yi
amfani da tsohuwar hanya na
kwafe lambobinka a cikin SIM
ɗinka sannan ka saka shi cikin
wayar android ko tablet sannan ka kwafe shi cikin ta.
(3) Mene ne dalilin da ya sa
wayoyin android ba sa k**a
da juna?
Kamfanin google su s**a kirkiri
manhajan Android amma kuma sai s**a bai wa kamfanonin da
suke yin waya damar su yi
amfani da wannan manhajar a
cikin wayoyinsu. Saboda haka shi
ya sa kake ganin fuskokin da
kuma k**anninsu ya banbanta. Kamfanonin da suke da wannan
lasisi sun haɗa da kamfanin
Samsung da kuma kamfanin HTC,
wanda waɗannan kamfanonin
kowannensu, kera waya da kuma
kayan Kwamfuta yake yi. Saboda haka kowane ɗaya daga cikinsu
yana da damar ya yi irin kalar
waya ko kuma tablet da yake
ganin za ta amsu a hannun
abokanen cinikinsa.
(4) To yaya za a yi in samu android wacce ba ta waɗancan
kamfanonin ba?
Idan baka son ɗaya daga cikin
wayoyin da kamfanin HTC ko
Samsung suke yi, to ai kamfanin
google yana da tashi wayar mai suna NEXUS. Wanda aka fi sani da
Nexus 7 Tablet da kuma Galaxy
Nexus Phone. Waɗannan guda
biyu da manhajar da kuma
karafan da suke jikinsu duk
mallakar kamfanin google ne. Sannan kuma su waɗannan
wayoyi ko da wane lokaci
kamfanin google yana ƙoƙarin
inganta su ta wajen manhajin da
suke amfani da su, kasancewar
suna samun komai kai tsaye daga wurin google. Su kuwa sauran
wayoyi k**ar na HTC da
Samsung waɗanda suke amfani
da manhajar android s**an ɗauko
wani lokaci mai tsawo kafin a
waiwayi manhajar tasu, domin abu ne mai yawa da kuma faɗi da
kuma abubuwan da waɗancan
kamfanonin suke yi yana musu
yawa.
(5) Mene ne banbanci tsakanin
Home Screen da kuma App Drawer?
Shi App Drawer shi ne wurin da
za ka samu dukkanin application
da ka ɗaura wa android, an kira
wurin da Drawer k**ar yadda
malam Bahaushe ya sani da matsayin rumbu kasancewar nan
ne ake samun abubuwan da aka
ajiye a ciki. Saboda haka Adroid
suna da fallaye guda bakwai da
s**a baka damar ka fito da
dukkanin application da kake yawan aiki da su, domin samun
sauƙi. To, waɗannan application da
ka saka a kan wannan falle shi
ake kira da
Home Screen. Su
kuma application da baka son ganinsu a wannan fallen su kuma
suna cikin
App Drawer.
(6) Mene ne Widgets?
Widget k**ar yadda ake furta su
da Hauwa “wijet” suna da amfani matuka domin su ana amfani da
su wajen bayar da waɗan su
bayanai da kuma tattalin wutar
batirin android. Su k**ar hotuna
ne na waɗansu application da ka
saka a cikin Home Screen ɗin ka wanda za su riƙa faɗa maka
abubuwan da yake gudana
ƙarƙashin waɗannan application
da ka saka su a cikin wijet ɗin.
Misali wanda ya ɗauko application
na facebook ko twitter ko na gmail ya saka a cikin wijet to duk
sakon da ya shigo, ɗaya daga
cikin waɗannan application ɗin zai
ga matashiya kai tsaye wanda ba
sai ya buɗe shi application karan
kansa ba.
(7) Ina da abubuwan saurare a
itunes zan iya sauraronsu a
android dina?
Akwai wani software da ake kira
da doubleTwist yana aiki k**ar
yadda ka san Itunes yake yi. Saboda haka idan ka ɗaura shi zai
baka damar saukar da duk abin
da kake da su a Itunes zuwa
Android dinka.
By Sulaiman Ali Telecoms
WhatsApp Number +2348081888188

ASSALAMU ALAIKUM WARAHMATULLAHI TA ALA WABARAKATUHU.Ya'yan Uwanmu A MUSULUNCIN Ki/kayiwa Zuciyarka garan bawul da Wadann...
19/12/2017

ASSALAMU ALAIKUM WARAHMATULLAHI TA ALA WABARAKATUHU.

Ya'yan Uwanmu A MUSULUNCIN Ki/kayiwa Zuciyarka garan bawul da Wadannan
>
KAMAR HAKA :-
1 )
Waishin Zuciyar ka tana Kara tabbatar maka da cewa ANNABI Shine Sama da komai ?????
2 )
Koko tana darsa maka cewa za'a iya gwada wani da Shugaba ?????
WALLAHI ALLAH adukkan Halittun ALLAH babu wani KO wata da za a gwadashi da SHUGABA ( SALLALLAHU ALAIHI WASALLAM )
Kowaye to dan haka gwada wani da ANNABI (S.A.W.)
{{{ FASIKANCI NE }}}.
3 )
Ka Amsa Wannan ((( TAMBAYAR ))) Kokanemi Karin bayani a gurin Ma'abota sanin Hakkin SHUGABA.
------- HUKUNCIN Wanda s**a gayawa SHUGABA KALMAR ZAGI [[[ KISANE ]]]
MENENE hukuncin wa'yanda basa son ayi Hukuncin kuma suke gaba da wa'yanda suke damuwa da ayi HUKUNCIN ?????
,
,
,
ALLAH YASANI BAZAMU TABA GAYA MUSU KYAKYKYAWAR KALMA BA KUMA WANDA YACE MUNA XAGI KO MUNA ASHAR SHIMA ZAICI UWARSA INDAI AKAN WANNAN NE AKE CEWA MUNA XAGIN WALIYI KO FADA MASA MAGANA

KUMA SAKO AFADAWA DUNIYA IDAN KANA KISHIN ANNABI BAKAYI WANI ABU AKAIBA KODA TURAWANE YAN UWA SUGANI NI SULAIMAN ALI NACE ALLAH YALA ANCEKA YA TSINE MAKA/KI

KUMA AGAYAWA DUK MAI KISHIN SHUGABA TO YARABU DA WA'YANNAN MUTANEN A YANKE ABOTA DASU A DAINA ZAMA WAJE DAYA DASU A DAINA AUREN YA'YANSU A DAINA KASUWANCI DASU DOMIN HAKAN KISHIN ANNABI NE
KUMA AYI TA ISTIGIFARI DOMIN ALLAH YA DAUKE MANA DUKKAN ANNOBA YA MAYAR DA ANNOBAR KAN MASU TABA MUTUNCIN ANNABI
DA MASU GOYAN BAYANSU DA MUNAFUKAI WADAN DA BASU BAYYANA KANSUBA AMMA SUSANI MUNSANSU SUNA NAN SUNA ZAGIN MASU NEMAN HAKKIN SHUGABA ( S.A.W )
SUNA FAKEWA DA CEWA HAKAN KIN WALIYAINE SANNAN SUNMANTA DUK WANDA AKE GWADASHI DA SHUGABA { S.A.W. } MARTABAR SA TANA FADUWA .
HADA WANI WALIYI DA ANNABI YANA JAWO ALLAH YAYI FUSHI DA WALIYIN DA KUMA MASU GWADASHI DA SHUGABA (S.A.W.)
AKIYAYE AKIYAYE
,
,
SAKO NE HAR FADAR SHUGABAN KASA
MUHAMMADU BUHARI DAMA SARKIN SAUDIYA
ASHIRYE MUKE FA MUDAU MAKAMI MATUKAR XA A DINGA TABA MARTABAR ANNABI MUNJIMA DA SABAWA DA MUTUWA INKUMA AKWAI WANI ABU SAMADA MUTUWA TO MUNA JIRA WANDA YAFASA ALLAH YA TSINE MAI KOMU KOKU
,
,
,
SAKO DAGA
MAI DUBIN ISA ISLAMIC FOUNDATION
SARKIN YAKIN MAI DUBIN ISA
SULAIMAN ALI ZANGO
08081888188

all friends
10/10/2017

all friends

12/08/2017

hello brothers

18/07/2017

_*ANA IYA LEKEN ASSIRIN MUTUN TA
WAYA KUWA???*_
~||||||||||||||||||||||||||||||||||||~
```DAGA DARASINMU AYAU GROUP
WHATSAPP
08149993999 TARE DA MAS'UDU DAN
MASANI SHINKAFI```
~||||||||||||||||||||||||||||||||||||~
Amsa itace ‘e’ ana iyawa, domin mafi
yawancin mutane da ke amfani da
manyan wayoyi (smartphone) irin su
Android, iPhone, iPad da mk**antansu
tamkar kusan tsirara suke. Akwai
mutane da kan iya ganin sirrin ka ta
cikin wayar taka daga nesa. Babban abu
ma shi ne akwai waɗansu Apps da idan
ka sake ka sa su a wayar ka za su fara
aiki a boye (background) kai tsaye har
ma da amsa kuwar ɗin wayar ka
(microphone) ta ɗaukar maganganun
ka tana aika wa da su. Ƙarami daga
cikin irin waɗannan Apps ɗin shi ne
stealthGenie (spyware) yakan zama
abin da ake cewa Trojan kuma yana iya
aiki da iOS dinka, kai hasali ma yakan yi
amfani a Android da Blackberry ya aika
taswirar (geolocate) ɗinka ya kuma
saurari maganganunka, saƙonnin rubutu
(text messages) da hotunan ka ya aika
da su kowane lokaci.
Wani kamfanin da ya ke yin irin
waɗannan Apps sun taɓa yin alfaharin
cewar suna da mutane (customers)
sama da dubu ɗari (100,000) duk da dai
hukumar tsaro a Amurka ta cafke shi
shugaban wannan kamfanin.
Za mu iya tunawa da maganganu da
ɗan leƙen asirin nan na Amurka wato
Edward Snowden da ya yi na cewa
gwamnatin Amurka tana leƙen asirin
cikin wayoyi, saƙonnin e-mail da
sauransu al’amuran intanet na mutane
da yawa a cikin duniya. Wannan
magana ta tsohon jami’in CIA ta
tabbatar mana cewar lallai NSA na
amfani da hanyoyi daban-daban wajen
neman sirrin mutane.
Akwai wani Apps da ake kira da suna
Angry birds shi ma yana ɗaya daga
cikin Apps da ake amfani da shi wajen
leken asirin.
Saboda haka nake ganin ma cewar yan
uwa su kiyaye akan wash sirrikan
musaman ma kiyayewa zuwa banɗaki
da wayar (smartphone) domin tana iya
maka tonan silili.
Masu bincike a jami’ar Stanford sun
gwada wani Apps (Gyrophone) domin
tabbatar da irin wannan zargin kuma
sun ta gano cewar lallai amsa kuwar
waya (microphone) kan iya aika
sautinka, kai har ma da gano wanda ke
yin magana. Wannan Apps na da ƙarfin
tafiya a iska na 80 – 250 Hz a kan iska.
Sun gano da tabbatar wa duniya cewar
amfani da wannan Apps (Gyrophone)
za a iya gano mai magana dama mai
amsa maganar. Sun gwada a kan wayar
Android ya yi aiki yanzu ma har sun fara
gwadawa a kan iPhone.
Wasu jami’oi ma k**ar Citizen lab a
jami’ar Toronto sun yi wannan gwajin
da gano masu leƙen asiri ta irin wannan
hanyar a ƙasar Italiya. An tabbatar
cewar masu leƙen asirin suna amfani
da GPS tracker na amsa kuwarka da
zaran ka hau yanar gizo (internet) ta Wi-
fi.
Binciken ya nuna cewar akwai manyan
kwamfutocin da ake amfani da su wurin
leƙa sirrin mutane (computer servers)
sama da guda 350 a ƙasashen duniya
guda 40 da ake amfani da su. Abin
tambaya dani DAN MASANI nake a nan
shi ne, Yan uwa sun san da haka kuwa?
Saboda haka ka lura domin wayar ka ta
smartphone da kake tunƙaho da ita
kake maƙale da ita kullum musamman
ma'amalar wasu abubuwa na harkar
islamiyyah, da guje wa kaɗaici mai tona
ma ka asiri ce. Saboda haka abin sai
addu’a da kuma kiyayewa nusamman
mu yan uwa.
* DAGA MAS'UDU DAN MASANI
SHINKAFI*
_KU KASANCE DAMU A DARASINMU
AYAU GROUP AMMA KAR KU MANTA_

17/01/2015

Assalamu Alaikum

Rahotanni daga Maiduguri babban birninjahar Borno da ke arewacin Najeriya nacewa, wanni bam ya tashi a babbar kasuwata M...
10/01/2015

Rahotanni daga Maiduguri babban birnin
jahar Borno da ke arewacin Najeriya na
cewa, wanni bam ya tashi a babbar kasuwa
ta Monday market da ke tsakiyar birnin.
Lamarin ya hallaka mutane, ya jikkata wasu
dadama.
Wani jami'in asibiti a birnin ya shaidawa
sashen Hausa na BBC cewa: "an kawo musu
gawarwaki 15 kuma wasu dadama sun samu
raunuka."
Jami'in ya kuma ce suna bukatar taimakon
jini, don haka yayi kira ga jama'a da su je
su bada gudunmawar jinin.
Ana samun bayanai masu cin karo da juna
akan tashin bam din.
Yayinda wasu ke cewa wata yarinya ce ta yi
kunar bakin wake, wasu na cewa dasa bam
din aka yi.
Ko watan Yulin bara ma wani bam da ya
tashi a kasuwar ya kuma hallaka mutane 18
a birnin.
A jihar Yobe ma mai makwabtaka da Borno
ma wani bam ya tashi a ofishin 'yan sanda a
garin Potiskum.
Rohotanni sun ce a kalla jami'an 'yan sanda
biyu sun rasa rayukansu, kuma wasu biyar
sun samu raunika.
Ya zuwa yanzu dai babu wata kungiya data
dauki alhakin kai harin.

10/01/2015

Kungiyar Amnesty International ta nemi a
binciki kisan gillar da aka yi zargin 'yan
Boko Haram sun yi a garin Baga na jihar
Bono.
A wata sanarwa da kungiyar ta fitar, ta
bayyana damuwa game da rahotannin kisan
gillar da ake zargin 'yan kungiyar ta Boko
Haram sun yi wa fararen hula masu matukar
yawa.
Amnesty International ta yi kira ga gwamnati
Najeriya da ta gudanar da bincike kan
wannan zargi.
Rahotanni dai na cewa dubban mutane aka
kashe a harin nan Baga, wanda aka kai tun
daga ranar Asabar ta makon jiya.

Hausa24KISAN KARE DANGI A BAGA: Sama DaMutane 2000 Za Su Iya Rasa Rayukan SuWani kisan kare dangi da 'yan kungiyar BokoH...
10/01/2015

Hausa24
KISAN KARE DANGI A BAGA: Sama Da
Mutane 2000 Za Su Iya Rasa Rayukan Su
Wani kisan kare dangi da 'yan kungiyar Boko
Haram s**a kaddamar a garin Baga, na jihar
Borno cikin sa'o'i 72, ya yi mummunar barnar
da tarihin kafuwar kungiyar ba a taba ganin
mak**ancinsa ba.
Kamfanin dillancin labarai na AP, ya rawaito
cewa watakila sama da mutane 2000 za su iya
rasa rayukan su, sanadiyar harin da aka yi wa
mutane kisan kiyashi.
Bayanai sun nuna cewa kusan kwanakin biyu
kungiyar ta shafe tana barin wuta a yankin,
wanda yayi sanadiyar shafe kauyuka 16 daga
doron kasa.
Sai dai wani abu da ya bawa kowa mamaki,
har zuwa yanzu kafafen yada labaran cikin
gida Nijeriya sun yi gum da bakin su kan
faruwar al'amarin, har sai da kafafen yada
labaran kasashen duniya s**a fara fitar da
labarin, a bangaren gwamnati har yanzu
shugaban kasa ko shugbagan rundunar tsaro
ta kasa babu wanda yace wani abu.
Tuni jam'iyyar adawa ta APC da dan takararta
na shugaban kasa, Janar Muhammadu Buhari
sun fitar da jawabai kan al'amarin, inda s**a
jajintawa mutanen da harin ya rutsa da su,
tare da daukar alwashin irin haka ba zai taba
faruwa ba karkashin mulkin jam'iyyar.

Address

Yakasai

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Abba ali Commander - SAC posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Share