03/04/2022
Aslm Yan uwana Muslim barka da war HK gawata Tina tarwa danake son yimàna a kan sahur,
SAHUR DA FALALARSA:
Sahur shi ne abincin da musulmi ke ci a karshen rabin kashin daren azumi, kafin bullowar alfijiri. Annabi (S.A.W) ya yi umurni da sahur domin bambamtawa tsakanin azuminmu da azumin ma' abuta littafi (Yahudawa da Nasarawa). Manzon Allah (S.A.W) ya ce "Bambancin azuminmu da na ma'abuta littafi (Yahudu da Nasara) shi ne cin abincin sahur".
Akwai albarka a cikin yin sahur, wannan kuma ya zo a hadisai masu yawa, daga cikin su akwai hadisin Salman (R.A) ya ce: "Manzon Allah (S.A.W) ya ce, "Ana sanya albarka a cikin abubuwa uku, daga cikin su akwai Sahur" da hadisin Abu Huraira (R.A) ya ce; "Manzon Allah (S.A.W) ya ce "Lallai Allah (S.W.T) Ya sanya albarka a cikin sahur”. Wani Sahabin Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare sa ya ce; "Na shiga wurin Manzon Allah (S.A.W) a lokacin yana Sahur, sai ya ce; "Lallai (shi sahur) albarka ce wadda Allah (S.W.T) ya ba ku ita, kada ku yi wasa da ita" Malamai sun tabbatar da cewa an so a jinkirta yin sahur sai kusan bullowar alfijiri, saboda Manzon Allah (S.A.W) da Zaid ibn Thabit sun yi sahur, lokacin da s**a kare, sai Annabi ya tashi zuwa sallar asuba ya yi sallah. Anas dan Malik ya ruwaito daga Zaid bn Thabit, (R.A) ya ce: "Mun yi sahur tare da Manzon Allah (S.A.W) sannan ya tashi zuwa Sallah. Anas ya ce wa Zaid ibn Thabit, daga kiran sallah zuwa sahur wane lokaci ne ke tsakaninsu? ya ce, gwargwadon (tsawon) karanta aya hamsin. Nagode D Al Ameen Yola.