26/04/2023
Yadda Zaka Zauna Da Masu Maka Hassada
A kullum mutanen dake maka hassada mutane a kullum burinsu suga sun bata maka duk wani shirinka na rayuwa.
Masu maka hassada ba lalle bane sai mutanen da s**a sanka ko ka sansu ba. Haka nan kawai mutum zai wayi gari yaji ya tsaneka ba tare da wani hujja ba kuma kila sunanka kawai yake ji ko hoton ka bai taba gani ba. Kamar yadda ake samun wasu dake jin sonka ba tare da sun sanka ba.
Ga wasu dabarun zama da mutane masu maka hassada domin samun kanka cikin walwalar da bazasu taba ganin gazawarka ba.
1: Duk yadda masu maka hassada zasu yi kada ka nuna musu ma kasan suna yi. Duk irin zagi ko bakaken maganganun da zasu rika jefo maka kada ka bata lokacinka wajen maida musu martani.
2: A kullum masu maka hassada neman gazawarka ko laifin ka suke yi domin ka kaskantar da kanka wajen nuna kayi kuskure ko ka gaza. Kada ka taba basu damar haka. Kada amince da laifin da bakayi ba saboda matsi ko takuran masu maka hassada.
Su ba suna neman kuskurenka bane domin su baka shawara ka gyara sai domin su nunawa duniya ka gaza.
3: A duk lokacin da masu maka hassada suke kokarin yada gazawarka. Kai kuma kayi kokarin yada ni'imar da Allah Ya maka da kake masa godiya akansu.
Shi mai hassada yana so yaga wanda yake yiwa hassada ya butulcewa Allah kamar shi. Don haka bazai taba fadin wani abu naga mai kyau ba, wannan yasa da zaran yaga kana lissafa irin ni'imar da Allah ya maka zai rasa kima a inda yake kokarin bataka.
4: A kullum kayi kokarin kirkiro wani nasara ko ci gaba da ka samu a wannan ranar yadda sakon wannan nasaran zai isa ga mai maka hassada.
Babban bacin ran mai maka hassada shine yaji ko yaga kana samu daukaka ko ci gaba. To koda na burga ne, yi kokarin ganin a kullum ka cusa masa bakin ciki da wani abu da zaka nuna ya sameka na alheri.
Kayi duk iya yinka kada ya rika jin wani labari mara dadi akanka. Idan ma yana binka a social media ne zaka ga da kansa ya cireka cikin abokansa saboda ba irin labaran da yake son ji akanka ba kenan.
Idan kuma a wani majalisa yake samun labarin ci gabanka zai dauke kafa ya daina zuwa wajen.
5: Ko da dakika guda kada ka bari mai maka hassada ya Bata maka rai. Ka sani kaine ke gaba da shi.
Duk mutumin da ba a masa hassada baida amfani a cikin al'uma. Ba a yiwa mutum hassada har sai idan ya dara wasu da wani abun da yake dasu basu dasu. Hakan mallakan abu ko da kuwa baiwa ne ba karamin nasara bane a rayuwar mutum.
Don haka kada dabi'u ko halayen masu maka hassada yasa ka kara ka zama ka kasa ci gaba da abubuwan da ka saka a gabanka.
Allah Ya rabamu da ciwon hassada.
✍️Tonga Abdul