04/11/2025
Fitacciyar ‘yar jarida daga Amurka, Kim Iversen, ta bayyana cewa maganganun da ake yadawa cewa Amurka tana nuna damuwa ne da halin Kiristoci a Najeriya, ba shi ne ainihin dalilin tashin hankalin da ake gani ba.
A cewar Kim, dangantaka mai karfi tsakanin Najeriya da kasar China, musamman ta fuskar Belt and Road Initiative, ita ce ke tada hankali a Washington.
Ta ce, tun daga farkon shekarar 2025 zuwa yanzu, Najeriya ta sanya hannu kan yarjejeniyoyin gine-gine da s**a kai darajar sama da dala biliyan 21, wanda hakan ke nufin kasar za ta kasance daya daga cikin kasashen Afrika da s**a fi cin gajiyar shirin Belt and Road daga shekarar 2026 zuwa 2030.
Kim ta kara da cewa, Amurka tana lura da irin yarjejeniyoyin da Najeriya ke kulla da China a bangaren mak**ashi, masana’antu, da hanyoyin sufuri — ciki har da shirin gina hanyoyin jirgin kasa tsakanin jihohi, wanda ke kara dankon zumunci tsakanin kasashen biyu.
A cewarta, irin wannan ci gaba yana sa tasirin Amurka a nahiyar Afrika ya ragu, don haka wasu daga cikin manyan masu ruwa da tsaki a Amurka na ganin tada hankula a Najeriya a matsayin hanya ta dakile wannan shiri.
Kim Iversen ta kammala da cewa, maganar kare Kiristoci da Amurka ke ta ambata wata hanya ce kawai da ake amfani da ita don samun hujjar tsoma baki, yayin da ainihin manufar ita ce hana China da Najeriya cimma manyan nasarori a fannin tattalin arziki da raya kasa.