Sabon Gari Local Government Market Association

Sabon Gari Local Government Market Association Contact information, map and directions, contact form, opening hours, services, ratings, photos, videos and announcements from Sabon Gari Local Government Market Association, Business service, muh'd iyande plaza shop 35/36 sabon gari main market zaria, Zaria.

Assalamu Alaiku Muna sanarda yan kasuwa cewa Sakamakon taron da akayi a office din hakimin sabon gari tare da dukkan ban...
17/05/2023

Assalamu Alaiku

Muna sanarda yan kasuwa cewa

Sakamakon taron da akayi a office din hakimin sabon gari tare da dukkan bangarorin yan shuwagabannin kasuwa kamar haka

1) kamfanin triple a Homes masu gina kasuwa

2)shuwagabannin kasuwar sabon gari market union

3) police station kasuwar mata division

4) sarkin kasuwar sabon gari

5) ban garen kungiyar izala

6) ban garen kungiyar darika

Sakamakon korafi da aka kaima hakimin sabon gari akan yawan basa shago a cikin kasuwa a yi sata

Shiyasa hakimi yakira taron masu ruwa da tsaki na kasuwar don ganin an kawo karshen wannan matsalar

Don haka daga yanzu za'a rinka bude kasuwa daga karfe 7am nasafe zuwa 6pm na yamma kuma dokar tafara aiki nan take

Muna bada hakuri na rashin sanarwa da wuri

Sanarwa daga Aminu mai tsada p.r.o sabon gari market Association

05/02/2022

INNALILLAHI WA INNALILLAHIR RAJIUN

muna amfani da wannan damar don jajantawa sakkwatawa mazauna kasuwar sabon gari zaria bisa iftila'in da yafadawa yan uwansu dake garin (AMBARURA)

wanda yan fashin daji s**a shiga garin kuma s**a kashe mata da yara Sannan s**a sace wasu s**a tafi dasu daji don neman kudin fansa

Muna fatan wanda s**a mutu Allah yajikansu da rahama

Sukuma wanda akayi garkuwa dasu Allah yafito dasu cikin Ameenci Ameen

Wannan sanarwace daga shuwagabañin yan kasuwar sabon gari zaria

Kai tsaye daga gidan gwamnatin jihar Kaduna tare da shugaban yan kasuwar sabon gari(Alh Ibrahim mai gold) da zaria metro...
03/02/2022

Kai tsaye daga gidan gwamnatin jihar Kaduna

tare da shugaban yan kasuwar sabon gari(Alh Ibrahim mai gold) da zaria metropolitan Administrator( haj hadiza Aliyu balarabe)

Don tattauna abinda yashafi kasuwanci da yan kasuwar

Allah ya dawo damu gida lafiya Ameen

✍ Aminu mai tsada p.r.o

A madadin yan kasuwar sabon gari zaria Muna taya Auwal Idris(D.c.o kasuwar mata police division) murnar samun karin girm...
02/02/2022

A madadin yan kasuwar sabon gari zaria

Muna taya Auwal Idris(D.c.o kasuwar mata police division) murnar samun karin girma daga d.s.p zuwa s.p

Bazamu manta da irin guduwar da kake bayarwa ba a kasuwar sabon gari ba

Wurin tabbatar da doka da zaman lafiya tsakanin yan kasuwa

Muna fatan Allah yakara girma da dauka Ameen mun gode

Sanarwa daga Aminu mai tsada p.r.o sabon gari Market Association

Muna sanarda yan kasuwarmu ta sabon gari da sukwantar da hankalinsu a kullum muna tsaye a kansu don ganin munsamarma al'...
13/11/2019

Muna sanarda yan kasuwarmu ta sabon gari da sukwantar da hankalinsu a kullum muna tsaye a kansu don ganin munsamarma al'umma sake a kan duk wani abu da yashafi kasuwarmu don haka zuwa anjima zamu kawomuku mahimman bayane akan wannan hoton da yake yawo a kasuwa muna godiya da irin hadin kan da ake bamu sanarwa daga Aminu mai tsada p.r.o

08/11/2019

Innalillahi wainnailaihir rajiun a madadin shuwagabanin yan kasuwar karamar hukumar sabon gari muna mika taaziyarmu ga dukkan al'umma musamman yan kasuwar sabon gari bisa rasuwar tsohon chairman Alh Abdulmumin mai agogo kuma zaayi janazarshi gobe insha Allahu Allah yajikansa ya gafarta masa Ameen sarnarwa daga Aminu mai tsada p.r.o sabon gari market Association

Sanarwa      sanarwa     sanarwaMuna sanar da dukkan yan kasuwar karamar hukumar sabon gari zaria kamar Kasuwar sabon ga...
04/11/2019

Sanarwa sanarwa sanarwa
Muna sanar da dukkan yan kasuwar karamar hukumar sabon gari zaria kamar
Kasuwar sabon gari
Kasuwar bayan gidan iya
Kasuwar yan katako
Kasuwar kwangila
Kasuwar samaru
Kasuwar basawa
Kasuwar yan lemo
Kasuwar muchia
Kasuwar p.z
Duk wannan kasuwannin suna karkashin shugabancin kungiyar yan kasuwar karamar hukumar sabon gari ne wanda Alh ibrahim mai gold shine shugabanta
Munbude group WhatsApp mai suna SABON GARI MARKET ASSOCIATION (SAGMA)Don kawo muku muhimman bayane da s**a shafi chigaban yan kasuwa. Domin shiga wannan group muna bukatar ka ajiye lambar wayarka don Allah wanda yasani yasanar da wanda bai saniba sanarwa daga (Aminu mai tsada P.R.O)

Kai tsaye wurin gudanar da zaben shuwagabannin kasuwar mata sabon gari zaria wanda shuwagabannin yan kasuwar karamar huk...
03/11/2019

Kai tsaye wurin gudanar da zaben shuwagabannin kasuwar mata sabon gari zaria wanda shuwagabannin yan kasuwar karamar hukumar sabon gari take gudanarwa wada (Alh Abbas sardauna)vice chairman 2 yake gudanarwa Allah yasa a tashi lafiaya Ameen

Kai tsaye muna tattaunawa da shuwagabannin yan kasuwar basawa karamar hukumar sabon gari don tattauna abinda yashafi tsa...
26/10/2019

Kai tsaye muna tattaunawa da shuwagabannin yan kasuwar basawa karamar hukumar sabon gari don tattauna abinda yashafi tsaron kasuwar da cigabanta saboda kudirin shugaban yan kasuwar karamar hukumar sabon gari Alh ibrahim mai gold na kawo tsaro da taftace kasuwanninmu daga zinace-zinace da sace-sace da akeyi sanarwa daga Aminu mai tsada p.r.o

Innalillahi wainna ilaihirrajiun A madadin shuwagabannin kasuwar karamar hukumar sabon gari ( SAGMA)muna mika taaziyarmu...
26/10/2019

Innalillahi wainna ilaihirrajiun A madadin shuwagabannin kasuwar karamar hukumar sabon gari ( SAGMA)muna mika taaziyarmu ga Alh umar salisu khalifa (vice chairman 3 sabon gari market Association )bisa rasuwar mahaifiyarsa kuma zaayi janaza da karfe 9:00am na safe a hayin ojo Allah yajikanta ya gafarta mata Ameen sanarwa daga Aminu mai tsada p.r.o

Kai tsaye a wurin taron shuwagabannin yan kasuwar karamar hukumar sabon gari don tattauna korafe-korafen da a kawo mana ...
19/10/2019

Kai tsaye a wurin taron shuwagabannin yan kasuwar karamar hukumar sabon gari don tattauna korafe-korafen da a kawo mana mussamman akan dokar fitow da tashi kasuwa.
Yanzu an maida dokar kamar haka
1)lokacin fitowa kasuwa ya koma 7:am
2)lokacin tashi yannan 7:pm
3)lokacin hana mata shigowa kasuwa yannan 6:30pm
Sannan kuma muna kira ga
1) teloli
2) masu zuwa kasuwannin kauye
3) masu kaiwa dare a kano
4) masu saida shayi
Da kuma sauran dukkan yan kasuwa cewa anfara saida forms nayin ID card #500 domin duk wanda yake da ID Card to zaisami lasisin shiga kasuwa a lokacin da akahana domin wata lalura idan takama domin karin bayani kakira wannan lambar 08137528262 sanarwa daga Aminu mai tsada p.r.o sabon gari market Association

Address

Muh'd Iyande Plaza Shop 35/36 Sabon Gari Main Market Zaria
Zaria
+234

Telephone

08137528262

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Sabon Gari Local Government Market Association posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Share