03/27/2026
TATTALIN ARZIKIN MAGANA: Me Kake Faɗa Wa Kanka?
"Shin ka san cewa babu wani babban maƙiyi da za ka taɓa haɗuwa da shi fiye da abin da kake faɗa wa kanka a asirce?
Kowace magana da ka faɗa tana zama iri (seed) da kake shukawa a cikin gonar kwakwalwarka. Idan kana cewa:
'Kasarmu ba daɗi, babu hanyar samun kuɗi.' — Kana shuka tsirowar talauci ne.
'Ni ba ni da sa'a a rayuwa.' — Kana gina katangar da za ta kare ka daga alherai ne.
Canza Salon:
Maimakon kace 'Ba zan iya saya ba', kace 'Yaya zan yi har na iya saya?'. Tambayar farko tana rufe kwakwalwa, tambaya ta biyu kuma tana buɗe hanyoyin neman mafita.
Kwakwalwarka tana bin umarninka ne. Idan ka ba ta umarnin gazawa, za ta gaza. Idan ka ba ta umarnin nasara, za ta binciko maka hanyar da ba ka taɓa tunani ba.
Darasi: Daga yau, karka sake faɗar wata magana mara kyau akan kanka, koda da wasa ne. Bakinka shi ne linzamin rayuwarka."